Mambobin majalisa sun fashe da kuka saboda yawaitar harin 'yan bindiga

Mambobin majalisa sun fashe da kuka saboda yawaitar harin 'yan bindiga

  • 'Yan majalisa sun fashe da kuka yayin zaman majalisa a jihar Katsina saboda yanayin tsaro
  • Sun koka kan yadda 'yan bindiga ke addabar mutanensu, da kuma hallaka wasu da dama
  • Sun yi kira ga gwamatin jihar da na tarayya cewa, ya kamata a kara kaimi wajen yakar 'yan bindiga

Katsina - 'Yan majalisar dokokin jihar Katsina biyu, a ranar Litinin, sun fashe da kuka a bayyane bisa yawan hare-haren da aka kai kwanan nan a cikin al'ummomin jihar ta Katsina, The Cable ta ruwaito.

Da yake magana ranar Litinin a zauren majalisar wanda kakakin majalisar Tasi’u Maigari ke jagoranta, Shehu Dalhatu-Tafoki, mataimakin kakakin majalisar, ya gabatar da wani kudiri na “mahimmantar da bukatar jama’a cikin gaggawa” kan matakin rashin tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mutum 14 Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Sake Kai Hari Jihar Kaduna

A cewar Dalhatu-Tafoki, mamba mai wakiltar mazabar Faskari, duk da kokarin gwamnatin tarayya da na jihohi, da hukumomin tsaro, har yanzu al’ummomi na fuskantar hare-hare.

Mambobin majalisa sun fashe da kuka saboda yawaitar harin 'yan bindiga
Taswirar jihar Katsina | Hoto: dailypost.ng
Asali: Twitter

Don haka, ya yi kira ga hukumomin gwamnati da abin ya shafa da hukumomin tsaro da su sake wata dabarun..

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Akwai matukar bukatar kayan aikin tsaro a cikin jihar ta yadda za su kara yawan wuraren aikin su a fadin jihar, musamman wuraren da abin ya fi shafa."
“Rundunonin da ke yankunan ba su isa ba. Ba za su iya shawo kan lamarin 'yan bindiga ba, duk da makudan kudaden da ake kashe musu.”

Ya kuma yi kira ga sauran jama’a da su ci gaba da addu’ar Allah ya dawo da zaman lafiya a fadin jihar.

A cikin gudummawarsa, Haruna Goma, dan majalisa mai wakiltar mazabar Dandume, ya ce an kashe mutane 11 a wani harin baya-bayan nan da aka kai kan al'ummomi biyu a Dandume, yayin da aka sace wasu mazauna da yawa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar

Yadda mambobin majalisa suka fashe da kuka yayin ba da labarin harin 'yan bindiga

A cewar kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN), yayin da yake ba da labarin abin da ya faru, dan majalisar ya fashe da kuka, sannan ya bukaci gwamnati da ta taimaka wa al’ummomin da abin ya shafa.

Hakazalika, Abubakar Mohammed, mamba mai wakiltar mazabar Funtua, shima ya fashe da kuka yayin da yake ba da labarin yadda 'yan bindiga ke kai farmaki kan al'ummomi a cikin watan da ya gabata, inda suka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu.

A nasa bangaren, dan majalisa mai wakiltar mazabar Batsari, Jabir Yusuf, ya bayyana kisan mutane 12 da aka yi kwanan nan a Duba, wata unguwa a Batsari, a matsayin abin takaici.

Bayan tattaunawa da 'yan majalisar, majalisar ta amince da kudirin tare da yin kira ga dukkan hukumomin da abin ya shafa da su yi kokarin magance matsalar cikin gaggawa ta hanyar tabbatar da tsaro a cikin al'ummomin da abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina

Zauren ya kuma yanke shawarar yin taro da 'yan majalisar tarayya daga Katsina, da kuma gwamnatin jihar, wajen kokarin magance rashin tsaro, in ji rahoton Punch.

Hakazalika zauren ya kara yanke shawarar ganawa da hukumomin tsaro da kwamitin jihar kan tsaro don nemo hanyoyin maido da zaman lafiya a yankunan da ke fuskantar kalubale.

Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon da mutum 50, sun hallaka mutum 4 a Maradun

A wani labarin, Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara a ranar Litinin 23 ga watan Agusta ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun hallaka mutum hudu tare da yin awon gaba da wasu mutum 50 a garin Goran Namaye da ke karamar hukumar Maradun.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, Muhammad Shehu, shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Gusau, babban birnin jihar a ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Muhammad Shehu, ya ce maharan, wadanda suka zo da yawansu, sun mamaye garin da tsakar daren ranar Lahadi, inda suka kashe mutum hudu tare da sace wasu 50.

Kara karanta wannan

Ku Tuba Ku Miƙo Makamanku, Ko Ku Fuskanci Ƙalubale, Sabon Kwamishinan Ƴan Sandan Zamfara

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.