Da Dumi-Dumi: Barayin da Suka Sace Malamai, Dalibai a Kwalejin Zamfara Sun Nemi a Tattara Musu Miliyan N350m

Da Dumi-Dumi: Barayin da Suka Sace Malamai, Dalibai a Kwalejin Zamfara Sun Nemi a Tattara Musu Miliyan N350m

  • Yan bindigan da suka yi awon gaba da wani adadi na ɗalibai a kwalejin Zamfara sun kira shugaban makaranta
  • Ɓarayin sun nemi a tattara musu kuɗin fansa miliyan N350m kafin su sako mutanen dake hannunsu
  • Kakakin yan sandan jihar, Muhammad Shehu, yace hukumar su ba ta da masaniya akan lamarin kuɗin fansa

Zamfara - Yan bindigan da suka sace malamai da ɗalibai a kwalejin fasahar noma da dabbobi dake Bakura, jihar Zamfara, sun nemi a basu miliyan N350m kuɗin fansa.

Da yake magana da Punch ta wayar salula, shugaban kwalejin, Alhaji Habibu Mainasara, yace barayin sun tuntuɓe shi ta wayar salula.

Yace yan bindiga sun nemi a ba su miliyan N350m kuɗin fansar mutum 20 dake hannun su a yanzun sannan su sako su.

Kara karanta wannan

Wani Mutumi Ya Mutu a Ɗakin Hotel Bayan Ya Shiga da Wata Mace Zasu Ji Dadi

Barayi sun nemi.kudin fansa
Da Dumi-Dumi: Barayin da Suka Sace Malamai, Dalibai a Kwalejin Zamfara Sun Nemi a Tattara Musu Miliyan N250 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Mainasara yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Sun faɗa mun cewa sai an basu kudin da suka bukata kafin su sako ɗalibai da malaman da suka kwashe a makarantar da nake jagoranta."

Wa zai biya waɗannan makudan kuɗi?

Sai dai shugaban makarantar bai fayyace cewa iyalan waɗanda aka sace ne zasu biya waɗannan kuɗaɗen ko kuwa gwamnatin jihar Zamfara, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara, Muhammad Shehu, yace sam hukumar yan sanda bata san ɓarayin sun nemi kudin fansa ba.

Shehu yace:

"Bamu da masaniya game da bukatar yan bindigan na kuɗin fansa amma muna iyakar bakin kokarin mu wajen kubutar da gaba ɗaya waɗanda aka sace."

Ba zamu bari a tada rikicin addini ba

A wani labarin kuma Ba Zan Bari a Tada Zaune Tsaye Ba, Gwamna Filato Ya Yi Kakkausan Magana Bayan Kashe Musulmai a Jos

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Cikin Gida Sun Kashe Basarake da Wasu 2 a Jihar Arewa

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, yace ba zai lamunci duk wani yunkuri na tada rikici a jiharsa ba ta hanyar yaɗa labaran ƙarya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Aƙalla matafiya 22 aka kashe a wani hari da aka kai kan hanyar Rukuba, karamar hukumar Jos ta rewa, jihar Filato.

Harin, wanda aka kaiwa wasu jerin motocin Bas dake ɗauke da mabiya addinin musulunci dake kan hanyarsu ta komowa Ondo bayan halartar wa'azi a Bauchi , ya bar wasu mutum 14 cikin rauni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262