Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 11, Sun Yi Awon Gaba da Wasu Sama da 40 a Jihar Zamfara

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 11, Sun Yi Awon Gaba da Wasu Sama da 40 a Jihar Zamfara

  • Wasu miyagun yan bindiga sun farmaki kauyen Randa dake karamar hukumar Maru a jihar Zamfara
  • Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutun 11 maharan suka kashe sannan suka sace wasu sama da 40
  • Wannan harin yazo kwanaki kaɗan bayan sace ɗaliban makarantar kwalejin fasahar noma dake Bakura

Zamfara - Wasu yan bindiga da ake zargin yan fashin daji ne sun kai hari kauyen Randa, yankin Ɗansadau, karamar hukumar Maru, jihar Zamfara, inda suka kashe mutun 11 kuma suka sace sama da 40.

Waɗanda maharan suka yi awon gaba da su, mafiyawancin su mata ne, iyaye masu shayarwa da kuma kananan yara.

Wani shaidan gani da ido ya faɗawa channels tv cewa maharan sun farmaki kauyen da yawansu ranar Talata da daddare misalin karfe 11:00.

Yan bindiga sun kashe mutum 11 a Zamfara
Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 11, Sun Yi Awon Gaba da Wasu Sama da 40 a Jihar Zamfara Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yace maharan na shiga garin suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi wanda hakan ya tilastawa mutane neman mafaka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Maharan sun kona gidaje

Legit.ng Hausa ta gano cewa bakwai daga cikin waɗanda aka kashe sun rasa ransu ne yayin da maharan suka cinna wuta a gidajen da suka ɓuya.

Shaidun suka ce:

"Jami'an tsaron sa kai sun kawo ɗauki inda suka fara musayar wuta da yan bindigan, amma yan fashin suka fi karfinsu."

Wane matakin yan sanda suka ɗauka?

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar, Muhammed Shehu, yace har yanzun basu samu rahoton harin ba, amma hukumar zata bincika.

A kwanan nan ne wasu gungun yan bindiga suka kai hari kwalejin koyar da fasahar noma da dabbobi dake Bakura, jihar Zamfara, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Yayin harin sun kashe masu gadi biyu da ɗan sanda ɗaya, sannan suka sace mutum 20, ɗalibai 15 da malamai 4, sai wani direba.

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ce Zata Lashe Zaben Gwamnan Anambra Dake Tafe, Uzodinma

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya yi ikirarin cewa babu ko tantama jam'iyyarsa ta APC ce zata lashe zaɓen gwamnan Anambra 2021.

Gwamnan wanda yake jagorantar kwamitin yakin neman zaɓe, yace farin jinin APC da nasarorin da ta cimmawa kaɗai sun isa su janye hankalin mutanen Anambra yayin kaɗa kuri'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel