Sauya Suna: NYSC Ta Gyara Dokar Matan Aure da Musulmi Suka Daɗe Suna Korafi

Sauya Suna: NYSC Ta Gyara Dokar Matan Aure da Musulmi Suka Daɗe Suna Korafi

  • Hukuma mai lura da matasa masu yi wa kasa hidima ta NYSC ta yi kwaskwarima ga wasu dokokinta da suka shafi matan aure
  • A sabuwar dokar, an cire sharadin saka sunan miji ga matan aure kafin a tura su hidima yankunan da mazajesu ke zama ko aiki
  • Legit ta tattauna da malamin addini, Ustaz Muhammad Abubakar domin jin matsayar addini kan amfani da sunan miji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar NYSC ta cire sharadin sauya suna ga matan aure kafin a tura su wuraren yi wa kasa hidima.

Rahotanni na nuni da cewa darakta mai lura tura matasa wuraren hidima, Abubakar Muhammad ne ya sanar da hakan.

NYSC matan aure
NYSC ta soke dokar amfani da sunan miji ga matan aure. Hoto: National Youth Service Corps
Asali: Twitter

Rahoton Jaridar Punch ya tabbatar da cewa a ranar 25 ga watan Nuwamba hukumar NYSC ta fitar da sanarwar.

Kara karanta wannan

Yadda malamai suka doki matashiya mai bautar ƙasa a Kwara, NYSC ta yi magana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An cire amfani da sunan miji a NYSC

Hukumar NYSC ta sanar da cewa an cire sharadin amfani da sunan miji ga matan aure a lokacin yin rajista.

Dama al'ummar Musulmi sun dade suna bukatar hakan kasancewar addini bai aminta da mace ta yi amfani da sunan miji ba, sai sunan mahaifi.

Daily Post ta wallafa cewa darakta mai lura da tura masu hidimar kasa wurare, Abubakar Muhammad ne ya tabbatar da soke dokar a Abuja.

"Hukumar NYSC ta amince da sauya dokar da ta tilastawa matan aure amfani da sunan miji kafin a tura su wuraren hidima.
Saboda haka, shugabannin NYSC a jihohi su san da cewa daga yanzu ba sai matan aure sun yi amfani da sunan miji ba.
Sai dai kuma dukkan sauran sharudan da suka shafi matan aure suna nan kamar yadda aka sani."

- Abubakar Muhammad

Bayan sauya dokar, NYSC ta buƙaci shugabanni da su tabbatar da an yi aiki da sabon hukuncin yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

An shiga jimami a Kannywood yayin da jaruma Rahama Sadau ta yi babban rashi

Legit ta tattauna da malamin addini

Wani malamin addinin Musulunci, Ustaz Muhammad Abubakar ya zantawa Legit cewa dama haramun ne mace ta canja sunan mahaifinta saboda ta yi aure.

Malamin ya ce NYSC ta yi abin a yaba mata kuma yana fata za ta dauki mataki a kan wasu abubuwan da suke karo da addini kamar saka mata sanya gajeren wando a sansanin da ake musu horo.

'Yan NYSC sun bukaci fara biyan N77,000

A wani rahoton, kun ji cewa masu yi wa ƙasa hidima da aka fi sani da ƴan NYSC sun koka kan rashin aiwatar da sabon alawus da gwamnati ta yi alƙawari.

Matasan sun roki gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da ta ɗauka saboda a halin da ake ciki N33,000 ba ta ɗaukar dawainiyarsu a wata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng