Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Matar Kansila da Jaririnta Dan Wata 7 a Zamfara

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Matar Kansila da Jaririnta Dan Wata 7 a Zamfara

  • Wasu yan bindiga sun kutsa gidan tsohon Kansila da tsakar dare sun sace matarsa da kuma jaririnta ɗan wata 7
  • Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:00 na daren ranar Laraba
  • Kwamishinan yan sandan Zamfara, Hussaini Rabi'u, ya bada umarnin tsaurara bincike da kuma kamo maharan.

Zamfara - Rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara tace wasu yan bindiga sun sace matar wani tsohon kansila, Babangida Ibrahim, da jaririnta ɗan wata 7, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya shaidawa hukumar dillancin labarai NAN cewa:

"Maharan sun kai hari gidan tsohon kansilan dake Damba yankin Gusau, babban birnin Zamfara, da misalin karfe 12:00 na dare ranar Laraba."
Yan bindiga sun kai hari gidan tsohon Kansila a Zamfara
Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Matar Kansila da Jaririnta Dan Wata 7 a Zamfara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ina Kansilan yake yayin harin

A cewar kakakin yan sandan jihar tsohon kansilan ya tsira da harbin bindiga a jikinsa kuma a halin yanzun ana bashi kulawa a asibiti.

Daily Nigerian ta ruwaito SP Shehu yace:

"Jami'an yan sanda na cigaba da gudanar da bincike da bibiyar yan bindigan domin kuɓutar da mutanen cikin koshin lafiya."

Kwamishinan yan sanda ya bada umarnin tsaurara bincike

Bayan samun rahoton kai harin, Mr. Shehu yace kwamishinan yan sandan jihar Zamfara, Hussaini Rabi’u, ya bada umarnin binciko yan bindigan da kamo su.

Shehu yace:

"Kwamishinan yan sanda, CP Husaaini Rabi'u, ya bada umarnin gaggawa na gudanar da binciken kwakwaf kan lamarin da kamo waɗanda suka kai harin."

A wani labarin kuma Babban Malamin Addini Ya Kwace Matar Dalibinsa Daga Zuwa Neman Albarkar Aure

Wani mutumi, Bright Ben, ya zargi babban faston cocin su ta General Overseer dake Eneka, karamar hukumar Obio-Akpor, jihar Rivers da yi masa kwacen mata.

Bright ya bayyana cewa lamarin ya fara ne daga lokacin da aka baiwa matarsa da sukai shekara 12 tare mukamin mai hidima ga coci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel