Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sako Daliban Makarantar Bethel Baptist Kaduna

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sako Daliban Makarantar Bethel Baptist Kaduna

  • Yan bindigan da suka sace ɗalibai a makarantar Bethel Baptist Kaduna sun sako karin dalibai 15
  • A baya dai barayin sun sako yara 28 daga cikin waɗanda suka sace bayan biyan miliyan N50m kuɗin fansa
  • Shugaban kungiyar CAN reshen jihar Kaduna, John Hayab, yace an sako karin 15 ranar Asabar da daddare

Kaduna - Yan bindiga sun sako ɗaliban makarantar sakandiren Bethel Baptist guda 15, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Idan zaku iya tunawa a bayan yan bindiga sun sako ɗalibai 28 daga cikin waɗanda suka sace ranar Lahadi 25 ga watan Yuli bayan an biya miliyan N50m kuɗin fansa.

Barayin sun sace adadin ɗalibai 121 a makarantar kamar yadda shugaban Baptist reshen Kaduna, Ishaya Jangado, ya bayyana, wanda shine ke jagorantar makarantar.

Yan bindiga sun sako karin daliban Bethel Baptist
Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sako Daliban Makarantar Bethel Baptist Kaduna Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shugaban ƙungiyar kiristoci ta kasa (CAN) reshen jihar Kaduna, John Hayab, yace yan bindigan sun sako ɗaƙibai 15 ranar Asabar da daddare, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwanda aikin tukin Keke Napep da koyarwa: Malamar makaranta ta ajiye karantarwa

Saura dalibai nawa a hannun ɓarayin?

Shugaban CAN ya kara da cewa yanzun sauran ɗalibai 65 ne suka rage a hannun yan bindigan.

Mista Hayab yace:

"Babu wani biki da zamu shirya na haɗa daliban da aka sako da iyayensu, don haka kowa yazo ya ɗauki ɗansa su tafi gida."

Zamu sako ɗaliban kashi-kashi

Yan bindigan su bayyana cewa zasu saki ɗaliban baki ɗaya amma rukuni-rukuni bayan sun saki rukinin farko na 25 a baya.

Rahotanni sun nuna cewa sai da aka biya kuɗin fansa na miliyoyin kuɗi kafin ɓarayin su amince zasu saki yaran da suka sace.

Shugaban Baptist na ƙasa, Israel Akanji, yace ba za'a biya ko sisi da suna kuɗin fansa ba domin sako daliban.

A wani labarin kuma Pantami Ya Bayyana Makudan Kudin da Ma'aikatarsa Ta Tattarawa Gwamnatin Tarayya Cikin Shekara 2

Kara karanta wannan

Allah ya yadda: Hotunan Jarumi kuma mawaki Garzali Miko tare da zukekiyar matarsa

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, yace ma'aikatarsa na taka muhimmiyar rawa a tattalin arzikin kasa

Pantami yace daga zuwansa ofis shekara biyu da suka gabata ICT ta samar da tiriliyan N1tr. A cewarsa, a wasu lokutan sai da gudummuwar ICT gwamnatin tarayya take iya biyan ma'aikata albashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262