Murna Ta Koma Ciki: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Yan Bikin Aure da Dama a Kwara
- Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mahalarta ɗaura aure yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Ilorin daga Ekiti
- Hakanan kuma wasu yan fashi sun sace mutun bakwai cikinsu harda fasto da matarsa a wani hari na daban
- Jami'an tsaro sun yi nasarar kubutar da wasu daga ciki kuma suka kame wasu da ake zargin suna da hannu a harin
Kwara - Aƙalla mutum 27, cikinsu har da yan bikin aure 7, Fasto da matarsa aka sace a harin yan bindiga biyu kan hanyar Kwara-Ekiti ranar Asabar da yamma, kamar yadda vanguard ta ruwaito
Majiyar yan sanda ya nuna cewa yan bindigan sun yi awon gaba da mahalarta ɗaura aure 7 yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Ilorin daga Kwara.
Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru a tsakanin hanyar Oke-Onigbin da Omu-Aran dake karamar hukumar Irepodun, jihar Kwara ranar Asabar .
Hakazalika, an kai hari na biyu ne a hanyar Ekan-Meje dake karamar hukumar Oke-Ero, jihar Kwara, inda aka yi awon gaba da fasto, matarsa da wasu da dama.
Wane mataki yan sanda suka ɗauka?
Kakakin yan sandan jihar Kwara, SP Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da kai harin sace mutane sau biyu, amma yace jami'an yan sanda sun kubutar da mutum 9.
A wata sanarwa da ya fitar da yammacin Lahadi, Okasanmi yace jami'an yan sanda sun kubutar da huɗu daga cikin yan ɗaura aure bakwai da aka sace.
Yayin da a hari biyu kuma jami'an sun kubutar da mutum 4 yayin da har yanzun ba'a gano inda fasto da matarsa suke ba.
Okasanmi yace:
"Hukumar yan sanda ta samu rahoton sace mutane guda biyu ranar Asabar, inda wasu yan bindiga suka tare motar Siena da ta fito daga Ekiti zuwa Ilorin, sannan suka tasa mutum 7 dake cikin motar zuwa daji."
"Nan take rundunar jami'ai ta musamman da ta haɗa da yan sanda, yan bijilanti, mafarauta suka bi sawun masu garkuwa zuwa cikin dajin kuma suka kuɓutar da mutum 4. A halin yanzun ana cigaba da kokarin kuɓutar da sauran."
"Da irin wannan dabarar jami'an suka sake ɗaukar mataki kan rahoton sace wasu a kan hanyar Ekanmeje/Ekiti, inda suka kubutar da mutanen banda fasto da matarsa."
Shin an kame yan bindigan?
Okasanmi ya kara da cewa yayin wannan aikin jami'ai sun samu nasarar kame wasu daga cikin waɗanda suka aikata lamarin.
Kakakin yan sandan yace a halin yanzun waɗanda aka kama suna taimakawa jami'an wajen gano inda sauran suke.
A wani labarin kuma Akalla Mutum 5 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Dakarun Sojoji Suka Fatattaki Yan Bindiga a Kaduna
Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa aƙalla mutum biyar aka kashe a wasu hare-haren da yan bindiga suka kai jihar.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwa shine ya bayyana haka, ymya kara da cewa dakarun sojoji sun dakile yunkurin kai harin.
Asali: Legit.ng