Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dalibar Wata Jami'a, Su Nemi a Tattaro Miliyoyi Kudin Fansa

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dalibar Wata Jami'a, Su Nemi a Tattaro Miliyoyi Kudin Fansa

  • Wasu miyagun yan bindiga sun sace ɗalibar jami'ar jihar Kwara, dake karatun jarida
  • Maharan sun tuntubi hukumar jami'ar, inda suka nemi a tattara musu miliyan N50m kuɗin fansa
  • Hukumar yan sanda reshen jihar, ta bayyana cewa an tura jami'ai na musamman domin kubutar da dalibar

Kwara - Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun sace ɗaliba dake karatun jarida a jami'ar jihar Kwara, Malete.

Punch ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 9:00 na dare, lokacin wasu mutane a cikin mota suka yi awon gaba da ɗalibar yar 200-Level.

Legit.ng Hausa ta gano cewa ɗalibar mai suna Khadijat Ishaq, ta na kan hanya tare da kawarta zuwa dakin kwanan su dake wajen makaranta yayin da aka farmaketa aka sace ta.

Jami'ar jihar Kwara
Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dalibar Wata Jami'a, Su Nemi a Tattaro Miliyoyi Kudin Fansa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Maharan sun nemi kudin fansa

Wata majiya ta shaidawa manema labarai cewa maharan sun tuntuɓi hukumar jami'a kuma sun nemi a tattara miliyan N50m kuɗin fansa.

Sai dai Daraktan yaɗa labarai na jami'ar, AbdulRazaq Sani, ya fitar da sanarwa cewa an sace ɗalibar ne a kan hanyar Okoru cikin garin Malete.

Sani ya kara da cewa hukumar makaranta tana aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro domin kubutar da ɗalibar kuma a kame maharan, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Wane mataki jami'an tsaro duka ɗauka?

A sanarwar da ya fitar, Sani yace:

"Kwamishinan yan sanda na jihar Kwara ya tura tawagar jami'an yan sanda masu yaki da satar mutane zuwa Malete domin su yi aiki tare da jami'an sa kai na yankin a kubutar da ɗalibar."

"Saboda haka ne, mataimakin shugaban jami'ar, Farfesa Mohammed Akanbi (SAN) ya yi kira ga mutanen jami'ar da su kula kuma su gaggauta kai rahoton abinda ba su yarda da shi ba."
"Hakanan ya shawarci ɗalibai su kula da wuraren da suke zaune kuma su san waye suke tare da shi."

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar, Ajayi Okasanmi, yace rundunar zata yi duk abinda ya kamata don tabbatar da kubutar ɗalibar.

A wani labarin kuma Gwamna Lalong Ya Gana da Shugaba Buhari Kan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai a Jos

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari , ya saurari bayanai kan kisan gillan da a kaiwa musulmi a Jos a rikicin da suka biyo baya daga gwamnan Filato, Simon Lalong, ranar Talata.

Bayan sauraron inda aka kwana game da lamarin, shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya ta hanyar ma'aikatar jin kai da walwala, zata tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel