Yadda Wasu Fusatattu Mutane Suka Tari Yan Bindiga, Suka Hallaka Daya Daga Ciki a Taraba
- Wasu mutane sun fusata sun tari yan bindigan da suka kawo musu hari a jihar Taraba
- Ɓarayin sun kai hari gidan wani hamshakin manomi a ƙauyen Jauro Manu, dake karamar hukumar Gassol
- Yayin fafatawa da ɓarayin, mutanen gari sun samu nasarar kashe wani ɗan Okada dake tare da ɓarayin
Taraba - Wani ɗan Okada da ake kira da suna Haro ya rasa ransa a ƙauyen Jauro Manu, ƙaramar hukumar Gassol, jihar Taraba, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Wanda ake zargin dai ya rasa ransa ne yayin da wasu fusatattun mazauna ƙauyen suka ci karfin masu garkuwa da suka kai hari ranar Litinin da dare.
Rahotanni sun bayyana cewa mazauna kauyen sun fito da yawansu lokacin da tawagar masu garkuwa suka kai hari gidan babban manomi, Irimiya Musa.
Wannan ba shine na farko ba
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani mazaunin ƙauyen wanda gidansa na daga cikin waɗanda aka kaiwa harin ya shaidawa manema labarai cewa wannan harin shine na uku.
Mutumin yace:
"A harin da suka kawo mana na farko, na samu nasarar tserewa amma sai da suka sace matata da kuma ɗiyata."
"Da farko sun sako ɗiyata inda suka bata layin waya ta bani domin mu tattauna da su game da kuɗin fansa."
"Ɓarayin sun cigaba da rike matata har tsawon kwana uku, amma a kwana na huɗu ta samu tserowa daga hannunsu."
Mutumin ya kara da cewa amma yayin da suka kai masa hari a karo na biyu ba su samu kowa a gidan ba.
Da aka tuntubi kakakin yan sanda na jihar Taraba, ASP Abdullahi Usman, yace yana cikin taro a lokacin.
Amma ya yi alkawarin zai sanar a hukumance da zaran ya samu cikakken bayani daga baturen yan sandan yankin.
A wani labarin kuma Abun Farin Ciki Gwamna Zulum Ya Jagoranci Sanya Marayu 5,361 Makaranta a Monguno
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ranar Laraba a garin Monguno, ya jagoranci saka marayu 5,361 da rikicin Boko Haram ya kashe iyayensu a makaranta.
Zulum wanda dakansa ya jagoranci ɗaukar bayanan Marayun, ya shafe kwanaki biyu yana gudanar da aikin.
Asali: Legit.ng