Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Jam'iyyar APC

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Jam'iyyar APC

  • Wasu yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC mai mulki na wata shiyya a jihar Neja ranar Asabar
  • Rahotanni sun bayyana cewa ɓarayin sun sace Aminu Bobi, shugaban APC na shiyyar C a gonarsa
  • Wata majiya ta kusa da wanda aka sace ta bayyana cewa Bobi kaɗai ɓarayin suka sace yayin da masu aiki a gonarsa suka tsira

Niger - Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC na shiyyar C, Aminu Bobi, a yankin karamar hukumar Mariga, jihar Neja, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa an sace Bobi ne yayin da ya je gonarsa domin sanya ido ga masu masa aiki ranar Asabar da yamma.

Wata majiya dake kusa da wanda aka sace ya bayyana cewa maharan sun farmaki gonarne a kan mashina shida, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam'iyyar APC
Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Jam'iyyar APC Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Mutumin ya kara da cewa kowane babur yana ɗauke da mutum uku, inda suna zuwa suka buɗe wuta kan mai uwa da wani.

Kara karanta wannan

Wata Amarya Ta Hallaka Angonta Kwanaki Kadan Bayan Sun Yi Auren Soyayya

Mutumin tace:

"Maharan sun kai hari gonar a kan babura shida, kowane babur yana ɗauke da mutum uku. Da isar su suka buɗe wuta domin tsorata waɗanda ke wurin."

Mutum nawa yan bindigan suka sace a harin?

Mutumin ya tabbatar da cewa Shugaban APC kaɗai yan bindigan suka yi awon gaba da yayin da ma'aikatan dake aiki a gonar suka tsira.

Duk wani kokarin tabbatar da lamarin daga rundunar yan sandan jihar Neja ya ci tura domin ba'a samu kakakin yan sandan Neja, DSP Wasiu Abiodun, ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

A wani labarin kuma Wata Amarya Ta Hallaka Angonta Kwanaki Kadan Bayan Sun Yi Auren Soyayya

An gano gawar wani ango a ƙasar Habasha kwanakin kaɗan bayan ɗaura masa aure a garin Nekemte dake yammacin Habasha, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa a halin yanzun an damke mutum 6 da ake zargin suna da hannu a kisan angon ciki harda amaryarsa.

Kara karanta wannan

Abinda Muka Tattauna da Jagoran APC Bola Tinubu a Birnin Landan, Gwamna

Asali: Legit.ng

Online view pixel