An Kama Kwararren Mai Garkuwa da Ya Sace Yarinya Ƴar Shekaru 4 a Kano

An Kama Kwararren Mai Garkuwa da Ya Sace Yarinya Ƴar Shekaru 4 a Kano

  • Rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Kano ta cafke wani matashi da ake zargi ya yi garkuwa da yarinya ƴar shekaru hudu da haihuwa
  • Rahotanni sun nuna cewa an kama matashin mai suna Saifullahi Abba ne bayan ya bukaci a ba shi kudin fansa har Naira miliyan uku
  • Kakakin ƴan sanda, Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa matashin ya tabbatar da aikata laifin kuma za a gurfanar da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Asirin wani kwararren mai garkuwa da mutane ya tonu bayan sace karamar yarinya ƴar shekaru hudu.

Ƴan sanda sun kama Saifullahi Abba ne bayan an samu korafi kan sace karamar yarinyar mai suna Nabila Zilkifilu.

Garkuwa
An kama wanda ya sace yar shekaru 4 a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka kama matashin ne a cikin wani sako da Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe dattijo mai shekaru 85 bayan karɓar kudin fansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama wanu mai garkuwa da mutane a Kano

Ƴan sanda sun samu nasarar cafke wani matashi mai shekaru 23 bisa zargin garkuwa da yarinya ƴar shekaru hudu.

Ana zargin Saifullahi Abba ya sace yarinyar ne a unguwar Daka Tsalle da ke karamar hukumar Bebeji a jihar Kano.

Mahaifin yarinyar mai suna Zilkifilu Abdullahi ne ya sanar da yan sanda cewa an sace ƴarsa kuma ana cewa ya biya kudin fansa N3m.

"Bayan samun korafi, kwamishinan 'yan sanda ya tura dakaru karkashin SP Aliyu Muhammad Auwal domin ceto yarinyar.
Bayan tsananta bincike, an kama Saifullahi Abba a ranar 28 ga Nuwamba a kauyen Lura na karamar hukumar Dawakin Kudi.
An ceto yarinyar da aka sace ba tare sa an cutar da ita ba, kuma an duba ta a asibitin Murtala an tabbatar tana lafiya."

- Abdullahi Haruna Kiyawa

An ruwaito cewa bayan Saifullahi ya bukaci a ba shi N3m, ya ce duk jinkirin rana ɗaya da aka yi sai an kara masa N1m.

Kara karanta wannan

An kama barawon buhunan shinkafa 150, ya sace kwalayen taliya 43 da man gyada

Haruna Abdullahi Kiyawa ya ce sun kama masu laifi da dama amma sun dade ba su ga kwararre kamar Saifullahi Abba ba.

An kama 'yan sara suka a Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Bauchi ta kai samame na musamman a kan ƴan daba da aka fi sani da ƴan sara suka.

A yayin samamen, an kama matasa da dama dauke da manyan makamai da ake zargin suna ta'addanci da su a sassan jihar Bauchi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng