Mahaifiyar SSG na jihar Bayelsa da aka sace ta kubuta daga hannun 'yan bindiga

Mahaifiyar SSG na jihar Bayelsa da aka sace ta kubuta daga hannun 'yan bindiga

  • Wasu 'yan bindigan da suka sace mahaifiyar sakataren gwamnatin jihar Bayelsa sun sako ta
  • Rahoto ya bayyana yadda iyalai, dangi da masu fatan alheri suka shiga farin ciki da dawowarta
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da dawowar matar daga hannun'yan bindiga a yau Lahadi

Bayelsa - Madam Betinah Benson, mahaifiyar Sakataren Gwamnatin Jihar Bayelsa (SSG), Rt. Hon. Konbowei Friday Benson, ta kubuta bayan shafe kwanaki 31 a hannun masu garkuwa da mutane.

Madam Benson, wacce aka yi garkuwa da ita a gidanta da ke tsohon gidan majalisa a Yenagoa a ranar 21 ga watan Yuli, an sake ta ranar Lahadi 22 ga watan Agusta da rana, Daily Trust ta ruwaito.

Wata majiya daga cikin iyali, da ta ki a bayyana sunanta, ta tabbatar da sakin matar mai shekaru 80 amma ba ta bayyana nawa aka biya a matsayin kudin fansa ba ko kuma inda aka sake ta.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke 'yar leken asirin 'yan IPOB masu kone-konen kayan gwamnati

Yanzu-Yanzu: An sako mahaifiyar na kusa da gwamna kwanasama da 30 bayan sace ta
Taswirar jihar Bayelsa | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Twitter

Iyalai, 'yan uwa da abokan arziki sun shiga murna da sako Madam Benson da 'yan bindiga suka yi.

Hakazalika, kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat ya tabbatar da sako matar ga jaridar Daily Trust.

'Yan sanda sun cafke 'yar leken asirin 'yan IPOB masu kone-konen kayan gwamnati

Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya (NPF) tare da hadin gwiwar sojoji da sauran jami'an tsaro sun cafke wata budurwa yar shekara 22 mai suna Gloria Okolie.

Hakan ya fito ne cikin wata sanarwar da mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Aremu Adeniran, ya fitar kuma Legit.ng Hausa ta samu a ranar Lahadi, 22 ga watan Agusta.

Adeniran ya lura cewa an kama Okolie ne saboda hada kai da ta yi a cikin jerin hare-haren da aka kai da gangan kan jami'an tsaro, wasu muhimman wurarenmallakin kasa ciki har da ofisoshin INEC da kashe jami'an tsaro a yankin kudu maso gabashin kasar.

Kara karanta wannan

Gwanda aikin tukin Keke Napep da koyarwa: Malamar makaranta ta ajiye karantarwa

Batun kame Sunday Igboho: An ci taran ministan shari'a Malami N50,000 akan Igboho

A wani labarin, Wata Babbar Kotun Jihar Oyo da ke zama a Ibadan ta tsawaita umurnin da ta bayar na hana hukumar tsaro na farin kaya daga kame dan awaren Yarbawa, Sunday Igboho, Punch ta ruwaito.

Mai shari'a Ladiran Akintola, wanda ya bayar da umurnin a ranar 4 ga watan Agusta a zaman da aka ci gaba da yi a ranar Laraba ya kuma ba da umarnin Malami ya biya N50,000 kasancewarsa wanda ake kara na farko.

An ba da umarnin biyan kudin daga Malami ne saboda shigar da martaninsa kan karar da Igboho ya shigar a kan lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel