Zamu Ceto Malamai da Daliban Kwalejin Bakura da Aka Sace, Matawalle Ya Yi Alkawari

Zamu Ceto Malamai da Daliban Kwalejin Bakura da Aka Sace, Matawalle Ya Yi Alkawari

  • Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya yi alkawarin kubutar da malamai da daliban da aka sace a Bakura
  • Gwamnan wanda ya nuna damuwarsa game da lamarin, yace alhakin gwamnatinsa ne ta ceto su
  • Ya kuma yi ta'aziyya ga iyalan waɗanda aka kashe yayin harin tare da fatan samun rahamar Allah

Zamfara - Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya nuna rashin jin dadinsa bisa sace ɗalibai 15 tare da wasu malamai a kwalejin fasahar noma da dabbobi dake Bakura, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Matawalle, a wata sanarwa da kakakinsa, Yusuf Idris, ya fitar ranar Litinin, yace alhakin gwamnatin jihar ne ta kubutar da su cikin koshin lafiya.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta kara tsaurara tsaro a dukkan makarantun dake faɗin jihar tun bayan sace ɗalibai mata a Jangebe.

Kara karanta wannan

Ba Zan Bari a Tada Zaune Tsaye Ba, Gwamnan Filato Ya Yi Kakkausan Magana Bayan Kashe Musulmai a Jiharsa

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle
Zamu Ceto Malamai da Daliban Kwalejin Bakura da Aka Sace, Matawalle Ya Yi Alkawari Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Matawalle ya ɗauki alkawari

Wani sashin sanarwar tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Gwamna ya umarci hukumomin tsaro su kara zage dantse kuma su ceto waɗanda aka sace, sannan ya yi alkawarin yin duk abinda ya dace domin ganin sun dawo gida cikin koshin lafiya."
"Matawalle, wanda ya yi matukar damuwa da harin yan bindigan, ya godewa Allah bisa ɗaukin da jami'an tsaro suka kai makarantar."
"Ɗaukin da jami'an tsaro suka kai cikin gaggawa ya sanya an kubutar da malamai uku cikin huɗu da maharan suka yi kokarin sacewa."

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Gwamnan ya kuma yaba da matakin bincike da jami'an tsaro suka ɗauka nan take domin tabbatar da an kubutar da waɗanda abun ya shafa, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Hakanan kuma Matawalle ya yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu kuma su taimakawa jami'an tsaro da bayanai don kubutar da ɗaliban.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Malamai da Dalibin Kwalejin Zamfara Sun tsero Daga Hannun Yan bindiga

Matawalle ya kuma mika ta'ziyyarsa ga iyalan waɗanda aka kashe yayin harin tare da fatan Allah ya karbi shahadarsu.

A wani labarin kuma An Sake Kashe Mutum 7 Bayan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai a Jos

Hukumar yan sanda na ganin wannan kisan na biyu yana da alaƙa da kisan gillan da aka yi wa matafiya a kan hanyar Rukuba a Jos.

Kwamishinan yan sandan jihar Filato, Edward Ebuka, shine ya sanar da kashe mutanen a karo na biyu ranar Lahadi da daddare jim kaɗan bayan taron tsaro a gidan gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel