Kasashen Duniya
A yayin da ake zaman makokin mutuwar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi, an ruwaito cewa girgizar kasa mai karfin 3.7m ta afku a yammacin kasar Iran a yau Litinin.
Shugaban juyin juya hali na kasar Iran, Ayatullah Ali Khamenei ya sanar da cewa za a yi kwanaki biyar ana zaman makokin shugaban kasar, Ebrahim Raisi da ya rasu.
Bayan mutuwar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi, mahukunta sun nada mataimakinsa, Mohammad Mokhber, a matsayin shugaban riko har zuwa a gudanar da zabe.
A yayin da aka tabbatar da mutuwar Ebrahim Raisi, shugaban kasar Iran da mukarrabansa a wani hatsarin jirgin sama, mun tattara abubuwan da ya kamata ku sani.
A yayin da duniya ke jimamin mutuwar shugaban Iran, Ebrahim Raisi, a hannu daya kuma, an kwantar da sarkin Saudiya, Salman bin Abdulaziz a asibiti saboda cutar huhu.
Rundunar sojojin Dimukradiyyar Congo sun sanar da dakile wani mummunan juyin mulki daga ƴan kasar da kuma mayakan kasashen ketare a yau Lahadi 19 ga watan Mayu.
Alhaji Aliko Dangote ya ce matatarsa za ta wadatar da Nahiyar Afirka da mai nan da watan Yuni da zamu shiga yayin da ƴan Najeriya ke fama da wahalar da mai.
Sabon shugaban kasar Senegal, Bassirou Faye ya kawo ziyara Najeriya yayin da ya sanya labule da Shugaba Bola Tinubu a fadar Aso Rock da ke birnin Abuja.
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya magantu yayin da kamfanin jiragen Emirates ya sanar da cewa zai dawo jigilar fasinjoji a Nigeria a watan Oktoba.
Kasashen Duniya
Samu kari