NSCDC ta damke Mai Safarar Mutane a Kano, Wasu sun Tsere

NSCDC ta damke Mai Safarar Mutane a Kano, Wasu sun Tsere

  • Hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC ta bayyana kama wani matashi a jihar Kano da ya kware wajen safarar mutane zuwa wajen kasar nan
  • Mutane 13 maza da mata hukumar da damke a kokarinsu ya fita zuwa makwabciyar kasar nan Kamaru ta iyakar jihar Maiduguri
  • Jami'in hulda da jama'a na hukumar reshen jihar Kano, SC Ibrahim Idris ya tabbatarwa manema labarai kamen, ya ce ana zurfafa bincike

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano-Hukumar tsaron fararen hula (NSCDC) ta samu nasarar damke wani mai safarar mutane, a kokarin fitar da su wajen kasar nan.

Matashin da a yanzu haka yake hannu tare da wasu mutane biyu Umar da Malam sun dade suna fitar da 'yan kasar nan kasashen ketare domin ci rani.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ceto mata da jariri daga hannun yan bindiga a Kwara

NSCDC
An kama mai safarar mutane a Kano Hoto: @NSCDCrops
Asali: Twitter

A sanarwar da Kakakin hukumar, SC Ibrahim Idris ya aikewa Legit Hausa, ya bayyana cewa sauran mutanen biyu da ake zargi sun cika wandonsu da iska.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda NSCDC suka kama matashin

Hukumar tsaron fararen hula (NSCDC) a jihar Kano ta bayyana cewa ta kama wasu mutane 13, maza da mata a kokarinsu na fita kasar Kamaru ta gabar Maiduguri, kamar yadda Pulse Nigeria ta tattaro.

Ya ce wasu daga wadanda aka kama sun maza da mata, amma wasu daga matan sun musanta cewa za kai su kasar Cameroon ne, kamar yadda Peoples Gazette ta wallafa.

Daya daga matan ma cewa tayi biki za su je Maiduguri da danta, yayin da wasu suka kara da cewa tafiya ce kawai ta hadasu da sauran.

NSCDC ta kama masu safarar fetur

Kara karanta wannan

Rana dubu ta barawo: 'Yan sanda a jihar Niger sun yi ram da barayin ATM

A baya mun kawo mu ku labarin yadda hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC ta damke mota dauke da litar man fetur 20 a kan titin Ibrahim Taiwo a Kano.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar a jihar, SC Ibrahim Idris ne ya tabbatar da kamen, inda ya ce kwarya-kwaryar bincike ya tabbatar da cewa za a yi safarar fetur din ne zuwa Katsina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.