"Daga Watan Yuni": An Shiga Murna Yayin da Dangote Ya Yi Albishir Kan Matsalar Mai

"Daga Watan Yuni": An Shiga Murna Yayin da Dangote Ya Yi Albishir Kan Matsalar Mai

  • Matatar Aliko Dangote za ta wadatar da Nahiyar Afirka da mai yayin da ƴan Najeriya ke fama da wahalar da mai
  • Dangote shi ya tabbatar da haka inda ya ce zuwa watan Yuni ko litar mai daya ba za a sake shigo da ita Najeriya ba
  • Attajirin ya ce matatarsa tana da wadatacce man da zai isa Nahiyar Afirka har ma a tura wani zuwa Brazil da Mexico

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Attajirin Dan kasuwa, Aliko Dangote ya yi wa ƴan Najeriya albishir kan matsalar mai a kasar.

Dangote ya ce nan da watan Yuni ko litar mai daya ba za a sake shigo da ita kasar ba saboda matatarsa za ta wadaci kasar.

Kara karanta wannan

Babban malamin Musulunci ya ja kunnen Ministar Tinubu kan hana aurar da mata a Niger

Dangote ya yi albishir ga ƴan Najeriya kan matsalar mai
Aliko Dangote ya ce daga watan Yuni ba za a sake shigo da mai Najeriya ba. Hoto: Bloomberg/Contributor.
Asali: Facebook

Yawan mai da Dangote ke samarwa

Attajirin ya bayyana haka ne a jiya Juma'a 17 ga watan Mayu a birnin Kigali na Rwanda tayin wani babban taro, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce a yanzu matatar tana samar da man dizal da kuma na man jirgin sama domin wadatar da al'ummar Najeriya.

Har ila yau, Dangote ya ce a yanzu man dizal da fetur da ya ke fitarwa zai wadaci Yammacin Afrika gaba daya, cewar rahoton Pulse.

Dan kasuwar ya ce kuma man jirgin sama da matatar ke samarwa zai wadaci Nahiyar Afirka baki daya.

Dangote ya yi albishir ga ƴan Najeriya

"A yanzu babu wani damuwa a Najeriya kan maganar shigo da mai kasar, nan da makwanni hudu zuwa biyar ko litar mai daya ba za a shigo da ita kasar ba."

Kara karanta wannan

Al-Mustapha ya tona asirin waɗanda suka lalata tsaro a Najeriya, ya kawo mafita

"Muna da wadataccen gas da zai isa Nahiyar Afirka ta Yamma da kuma man dizal da zai wadaci Yammaci da kuma Afirka ta Tsakiya."
"A bangaren man jirgin sama kuma muna da wadataccen kaya da zai isa Nahiyar Afirka gaba daya har ma a tura saura zuwa Brazil da Mexico."

- Aliko Dangote

Tinubu ya yabawa Dangote

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya yabawa attajiri Alhaji Aliko Dangote kan rage farashin man dizal da ya yi.

Tinubu ya ce wannan mataki da attajirin ya ɗauka zai taimaka wurin rage hauhawan farashin kaya da ake fama da shi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.