Jarumar BBNaija Kuma Ƴar Kasuwa Ta Bayyana Yadda Ta Samu N1.3trn Tana Barci

Jarumar BBNaija Kuma Ƴar Kasuwa Ta Bayyana Yadda Ta Samu N1.3trn Tana Barci

  • Matashiyar yar kasuwa kuma jaruma a shirin BBNaija, Kate Ka3na Jones ta rikita kafofin sadarwa da irin makudan miliyoyin daloli da ta samu a dare daya
  • Ka3na mai shekaru 29 daga jihar Rivers ta ce ta samu $900m yayin da take tsaka da barci ba tare da ta sha wahala ba
  • Ƴar kasuwar ta bayyana haka ne a shafinta na Instagram inda ta wallafa hotunan yadda aka siyar mata da wani kadara daga Birtaniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Jarumar BBNaija a shekarar 2020 kuma ƴar kasuwa, Kate ‘Ka3na‘ Jones ta rikita ƴan Najeriya kan daloli da ta samu a dare daya.

Kara karanta wannan

Lauyoyin Murja sun yi fatali da ita, sun fadi nadamar da suka yi a shari'arta

Jarumar BBNaija, Ka3na ta ce ta samu $900m tana cikin barci wanda ya kai kwatankwacin N1.3trn na kuɗin Najeriya a lissafin canjin yau.

Jaruma ta fadi yadda ta samu $900m yayin da take bacci
Jarumar BBNaija, Kate Ka3na Jones ta bugi kirji kan yawan miliyoyin daloli da ta samu. Hoto: @Ka3na.
Asali: Instagram

Ka3na ta bugi kirji game da arzikinta

Kate ta bayyana haka ne a shafinta na Instagram inda ta ce za ta kasance daya daga cikin masu arzikin matasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴar kasuwar ta kuma yada wani hoto da ke nuna an yi harkar kasuwanci ne da ya shafi siyar da kadara a birnin Landan da ke Burtaniya.

Matashiyar mai shekaru 29 yar kasuwa ce daga jihar Rivers wacce ta fafata a zango na biyar na BBNaija.

Ka3na ta auri ɗan Birtaniya, Mr. Jones

A shekarar 2020, Ka3na ta sanar da aurenta da wani dan Burtaniya mai shekaru 64 lokacin tana da shekaru 25 a duniya.

Kadarar da ta siyar na miliyoyin daloli na daga cikin arzikin mijinta wanda ya mutu mai suna Mr. Jones.

Kara karanta wannan

Niger: Ministar Tinubu ta yi amai ta lashe, ta dauki mataki kan aurar da mata 100

Sai dai wasu suna ganin tauraruwar karya tayi, ba ta samu irin wadannan kudi ba.

An watsawa mawakiyar Najeriya ruwan batir

A wani labarin, an ji cewa fitacciyar mawakiya kuma ’yar rawa ta gamu da tsautsayi bayan an watsa mata ruwan batir a jiki.

Mawakiyar wacce ‘yar Najeriya ce mai suna Korra Obidi ta gamu da tsautsayin ne yayin da ta ke tsaka da rawa a birnin London da ke Birtaniya.

Obidi ta wallafa faifan bidiyo a shafinta na Instagram a ranar Alhamis 11 ga watan Afrilu inda ta ce matashiyar ta kuma kai mata farmaki da wuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel