Shekara 1 a Ofis: 'Abin da Ya Sa Har Yanzu Tinubu Bai Nada Jakadu Ba', in Ji Minista Tuggar

Shekara 1 a Ofis: 'Abin da Ya Sa Har Yanzu Tinubu Bai Nada Jakadu Ba', in Ji Minista Tuggar

  • An bayyana karancin kudi a matsayin dalilin da ya sa har yanzu Shugaba Bola Tinubu bai nada wa Najeriya jakadu a kasashen waje ba
  • Ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce Najeriya na fuskantar babban kalubalen kudi da tabarbarewar tattalin arziki
  • Najeriya na da ofisoshin diflomasiyya 109, da ofisoshin jakadanci 76, da manyan hukumomi 22 da kuma kananan ofisoshi 11 a fadin duniya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce karancin kudi ne ya janyo tsaikon nada jakadu daga Najeriya zuwa kasashen waje.

Ministan na harkokin waje ya bayyana hakan ne a yayin taron baje kolin ayyukan ministocin Najeriya da aka yi a ranar Talata a Abuja.

Kara karanta wannan

An gina tasha mai otel, gareji da ofisoshi da za ta rika daukar motoci 5000 a rana

Gwamnatin tarayya ta yi magana kan nada jakadu
Ministan Tinubu ya fadi dalilin gaza nada jakadu bayan shekara 1 a ofis. Hoto: @YusufTuggar
Asali: Facebook

Tuggar yace gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta na fuskantar babban kalubalen kudi da tabarbarewar tattalin arziki, in ji rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yawan ofisoshin jakadun Najeriya a duniya

A ranar 2 ga Satumba, 2023, Shugaba Tinubu ya umarci dukkanin jakadun aiki da wadanda ba na aiki ba da ke tafiyar da ofisoshin Najeriya a kasashen duniya da su dawo gida.

Najeriya na da ofisoshi 109, da ofisoshin jakadanci 76, manyan hukumomi 22 da kuma kananan ofisoshi 11 a fadin duniya.

Rashin jakadu ya haifar da damuwa game da wakilcin diflomasiyya na Najeriya da tasirin ayyukanta a kasashen waje.

"Babu fa'idar nada jakadu a Najeriya" - Tuggar

Sai dai jaridar Vanguard ta ruwaito ministan ya ce ma’aikatar harkokin wajen kasar ba ta samun kudin da take bukata domin gudanar da aiki yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Manyan abubuwa 3 da suka faru a siyasar Najeriya daga 1999 zuwa 2024

Ambasada Tuggar ya yi nuni da cewa, babu wata fa'ida a nada jakadu alhalin babu isassun kudin tallafa wa tafiye-tafiyensu da kuma gudanar da ayyukansu a kasashen wajen.

Za a binciki korar ma'aikata 317 a CBN

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Ned Nwoko (PDP - Delta ta Arewa) ya nemi majalisar dattawa ta binciki yadda babban bankin Najeriya (CBN) ya kori ma'aikata 317.

Sanata Nwoko ya yi zargin cewa babban bankin ya yi rufa-rufa wajen aiwatar da korar kuma bai tuntubi masu ruwa da tsaki da suka hada da kungiyoyin kwadago ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel