Kasar Saudiya
Yayin da ake ci gaba da aikin hajji, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sake abin alheri ga maniyyatan jihar da ke kasar Saudiyya da kyautar riyal 100.
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya koka kan yadda alhazai suka tsinci kansu a Saudiyya a bana inda ya caccaki tsare-tsaren hukumar alhazai ta NAHCON.
Akalla ‘yan kasashen Jordan da Iran 19 ne suka mutu a lokacin aikin Hajji a kasar Saudiya sakamakon tsananin zafi. Ana kuma fargabar mutum 17 sun bace.
Hukumomi sun bayyana kame wasu mutum 18 da aka ce mahajjatan bogi ne a daidai lokacin da suke shirin shiga birnin Saudiyya ana kwana biyu Arfa a kasar.
Hukumomin kasar Saudiyya sun bayyana cewa za a fassara sakon da ke cikin huɗubar hawan Arafah ta bana zuwa harshen Hausa da wasu harsuna 19 na duniya.
Al'ummar musulmi sun kammala isa kasa mai tsarki yayin da a yau za a fara gudanar da aikin hajjin bana. Sai dai harin Isra'ila a a Gaza ya hana su zuwa Saudiyya.
Hukumar alhazan jihar Kwara ta tabbatar da rasuwar karin mahajjata daga jihar guda biyu, Salman Muhammad Alade da Ayishat Shuaib Ologele bayan fama da jinya.
Kasar Saudiyya ta bayyana cewa mahajjata 1,547,925 ne suka iso kasar domin aikin hajjin bana. Ma'aikatar lafiya ta shawarce su kan matsalar zafi a kasar.
Ministan harkokin cikin gida a kasar Saudiyya, Abdulaziz bin Saud ya bayyana cewa kasar ta shirya tsaf domin bada kariya ga mahajjata. Ya fadi haka ne a a jiya.
Kasar Saudiya
Samu kari