Kasar Saudiya
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya tura sakon gayyata ga shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan da mambobin kwamitinsa domin taro a Abuja.
Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun cafke wata hodar iblis da aka boye cikin littattafan addin don kai wa kasar Saudiyya.
Gwamnatin jihar Kebbi ta shirya tura dalibai zuwa kasar Saudiyya domin yin karatun digiri. Daliban za su yi karatu a fannin ilmin zamani da na addini.
Saudiyya ta saka 29 ga Afrilu a matsayin ranar ƙarshe da maniyyatan Umrah za su bar ƙasar. Wanda ya karya dokar zai fuskanci hukuncin tara da daurin watanni.
Fitaccen dan siyasa, kuma jigo a tafiyar Kwankwasiyya, Alhaji Buba Galadima ya bayyana cewa akwai kyakkayawar alaka a tsakaninsa da shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnatin Tarayya ta hannun ma'aikatar harkokin waje ta musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa an hana ƴan Najeriya shiga Saudiyya, ta ce labarin ba gaskiya ba ne.
Saudiyya ta karyata rahoton da ke cewa an hana kasashe 13 neman biza. Ta ce babu sabon takunkumi, sai dai ka’idar Hajji ga masu bizar yawon shakatawa.
Kasar Saudiyya ta bayyana ranar da za a gudanar da Sallah karama. Hakan na zuwa ne bayan an kammala duban watan Shawwal na shekarar 1446 bayan Hijira.
Kwamitin ganin wata ya bayyana lokutan da fadar sarkin musulmi ke duba ganin watan ƙasashen gabas kamar Saudiyya ko da ilimin falaki ya nuna ba za a ga watan ba.
Kasar Saudiya
Samu kari