Jihar Kaduna
Wasu tsagerun ‘yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun farmaki garuruwa a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna. Sun kashe mutum 9 tare da sace 35.
Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke GRA a Sabon Garin Zariya, ta umarci sayar da kadarorin tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna, Hon. Muhammad Sani Sha’aban.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar ya nuna damuwa kan yadda aka bar matasa babu aikin yi inda ya ce hakan babban barazana ce ga Najeriya.
Rundunar ‘yan sanda ta sanar da cafke wani tsohon sojan sama da ke safarar kayan sojoji ga ‘yan ta’adda musamman kasurgumi Bello Turji a jihar Kaduna.
Hukumar DSS ta tsare babban malamin Musulunci a Zaria da ke jihar Kaduna saboda kushe matakan Tinubu inda ya kwatanta shi da Buhari kamar Fir'auna da Hamana.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC watanni kadan bayan ya watsar da jami'yyar PDP mai adawa a jihar.
Shugaban karamar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna, Hon. Nasara Rabo, ya ba wa wani jami’in ‘yan sanda (DPO) mai suna Idris Ibrahim kyautar naira miliyan daya.
Jami'an Hukumar Hisbah na jihar Kano sun kama wata babban mota makare da kwalaben giya 8,600 da ta fito daga Kaduna sannan sun kama karuwa 15 a sassan Kano.
Bankin Duniya ya fitar da sabon rahoto kan yunwa da za a sake shiga a jihohin Arewacin Najeriya guda bakwai saboda rashin tsaro a wannan shekara da muke ciki.
Jihar Kaduna
Samu kari