Yan Bindiga Sun Kona Mutane 12 Har Lahira, Sun Kuma Babbake Gidaje 17 a Wata Jihar Arewa

Yan Bindiga Sun Kona Mutane 12 Har Lahira, Sun Kuma Babbake Gidaje 17 a Wata Jihar Arewa

  • A kauyen Gindin Dutse Makyali da ke, jihar Kaduna, 'yan bindiga sun halaka akalla mutane goma sha biyu a ranar Lahadi
  • Hakazalika a yayin harin ne 'yan bindigar suka kona gidaje 17 a harin da suka dauki tsawon sa’o’i suna cin karensu ba babbaka
  • Harin na zuwa ne bayan wani harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a Kwassam, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane shida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kaduna - Yan bindiga sun halaka akalla mutane goma sha biyu tare da jikkata wasu tara a sabon harin da suka kai kauyen Gindin Dutse Makyali da ke karamar hukumar Kajuru, jihar Kaduna.

Wani shugaban al’ummar yankin, Moses Musa, ya shaidawa Channels TV cewa harin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi a kusa da wani shingen binciken sojoji.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari jihar Arewa, sun tafka barna

Yan bindiga sun kai mummunan hari kauyukan Kajuru, jihar Kaduna
Yan bindiga sun kai mummunan hari kauyukan Kajuru, jihar Kaduna a ranar Lahadi. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Sai dai kuma rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda harin 'yan bindigar ya gudana a Gindin Dutse Makyali

Musa ya ce ‘yan bindigar sun mamaye garin ne da misalin karfe 5 na safe yayin da mazauna garin ke barci inda nan take suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Ya bayyana cewa mutane tara ne suka kone kurmus a cikin dakunansu, yayin da wasu tara suka samu raunuka daban-daban daga konewar wuta.

Shugaban al’ummar ya kuma bayyana cewa ‘yan bindigar sun kona gidaje 17 a harin da suka dauki tsawon sa’o’i suna cin karensu ba babbaka.

Hare-haren 'yan bindiga a Kudancin Kaduna na kara ta'azzara

Harin na ranar Lahadi a Kajuru na zuwa ne bayan wani harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane shida.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 9, sun sace tsohon daraktan CBN da wasu 34 a jihar Arewa

A cewar mai magana da yawun kungiyar Kudancin Kaduna (SOKAPU), Josiah Abraks, ‘yan bindigar sun kai hari a kauyen Kwassam a daren Juma’a.

Ya kuma ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutane 50 a wani harin da suka kai kauyen Sabon Layin a lokaci guda.

Abraks ya yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da jami’an tsaro da su kara kaimi kan yakar ‘yan bindigar da ke addabar al’ummomin Kudancin Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel