An Cafke Tsohon Sojan Sama a Kaduna Kan Safarar Kayan Sojoji Ga Bello Turji, Bayanai Sun Fito

An Cafke Tsohon Sojan Sama a Kaduna Kan Safarar Kayan Sojoji Ga Bello Turji, Bayanai Sun Fito

  • Rundunar ‘yan sanda ta yi nasarar cafke wani tsohon sojan sama kan zargin safarar kayan sojoji ga ‘yan bindiga
  • Ana zargin tsohon sojan da ya yi aiki a Kaduna da safarar kayan sojojin da sauran kaya ga kasurgumin dan ta’adda, Bello Turji
  • Ahmed Mohammed ya yi aiki da rundunar a Kaduna na shekaru biyar kacal kafin a kore shi kan wani laifi da ba a bayyana ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Rundunar ‘yan sanda ta sanar da cafke wani tsohon sojan sama da ke safarar kayan sojoji ga ‘yan ta’adda.

Rundunar ta ce an kama korarren sojan ne wanda ake zargi da samar da kayan sojoji da sauran kaya ga kasurgumin dan ta’adda, Bello Turji.

Kara karanta wannan

An ji kunya: Matasa masu karfi a jika sun kashe zuciyarsu, sun sace fanka a masallaci

An kama tsohon soja da ke safarar kayan sojoji ga Bello Turji
An kama Ahmed ne a Kaduna yayin da ya ke shirin tura kayan zuwa Zamfara. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Mene rundunar 'yan sanda ke cewa?

Tsohon sojan ya na sarafar kayan ne ga ‘yan ta’adda musamman da ke addabar al’umma a jihar Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda ake zargin, Ahmed Mohammed ya yi aiki da rundunar a Kaduna na shekaru biyar kacal kafin a kore shi kan wani laifi da ba a bayyana ba.

Kakakin rundunar ta kasa, Muyiwa Adejobi ya tabbatar da cewa tsohon sojan har ila yau, ya na safarar kayan ga Mushiri Abubakar wanda ke tura kayan ga ‘yan ta’adda daban-daban.

Kayayyakin da aka samu a hannun Ahmed

Adejobi ya ce mutanen biyu a baya sun kware wurin samar da kayan sojojin da wasu abubuwa ga Bello Turji da suka addabi jihar Zamfara.

Kakakin ya tabbatar da cewa an samu kayan sojoji 10 da huluna 2 da riguna uku da madaurin kugu biyu da sauransu.

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

An cafke su ne yayin da suke shirin daukar kayan daga Kaduna don safarar su zuwa jihar Zamfara ga ‘yan ta’adda.

‘Yan sanda sun cafke mata da zargin kisa

A baya, kun ji cewa rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta yi nasarar cafke wata mata da zargin kisan kai.

Ana zargin matar mai suna Cynthia da kisan Barakat yayin wata ‘yar hatsaniya da ta faru tsakaninsu.

Tuni rundunar ta tsare matar tare da fara bincike don tabbatar da gaskiya da kuma hukunta ta yadda ya dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel