Jihar Kano
An gurfanar da matar ne mai suna Hafsa bisa zargin ta yi wa mijinta dukan tsiya kan hira da 'yan mata a waya. Kotu ta kulle ta zuwa 11 ga watan Disamba, 2023.
Wani magidanci ya shigar da matarsa aure a gaban kotun shari'ar musulunci da ke Kano bisa zarginta da yin aure bisa aure. Ya nemu kotu ta raba auren.
Shugabannin NNPP sun bukaci ayi adalci a shari’ar zaben Kano ko kuwa rikici ya barke a Afrika, jagorori da magoya bayan NNPP su na cigaba da zanga-zanga da addu’o’i.
Mahaifiyar rikakken dan daba da ake nema ruwa a jallo a jihar Kano, ta yi ta-maza inda ta mika shi ga 'yan sandan jihar a ranar Talata. Ta nemi a yi masa afuwa.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya umarci kwashe dukkan mahaukata da ke yawo a titunan birnin da kewaye don ba su kulawa ta musamman a asibitocinsu.
l'ummar unguwar Kurna da ke birnin Kano sun fito zanga-zangar luma a safiyar ranar Laraba kan zargin 'yan sanda sun kashe wani matashi mai suna Salisu Player.
Yanzu haka masu zanga-zanga sun mamaye wasu tituna a jigar Kani domin nuna adawa da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP.
Kwamishinan 'yan sanda a jihar Kano, Hussaini Gumel ya umarci kama sifetan 'yan sanda da ya hallaka matashi a jihar yayin da ake zanga-zangar hukuncin kotu.
Sabon shugaban ma'aikatan jihar Kano, Musa Abdullahi ya gargadi ma'aikatan jihar da su guji zuwa wurin aiki a latti inda ya kafa musu lokacin zuwa aiki.
Jihar Kano
Samu kari