Kano: Kwamishinan ’Yan Sanda Ya Dauki Mataki Kan Sifetan da Ya Yi Ajalin Matashi Yayin Zanga-Zanga

Kano: Kwamishinan ’Yan Sanda Ya Dauki Mataki Kan Sifetan da Ya Yi Ajalin Matashi Yayin Zanga-Zanga

  • Yayin da ake cikin mawuyacin hali a jihar Kano na kisan wani matashi, kwamishinan yan sanda a jihar ya dauki mataki
  • Hussaini Gumel ya umarci kama sifetan dan sandan da ya yi ajalin wani matashi a Unguwar Kurna da ke Kano
  • Gumel ya bukaci al'ummar Kano da zauna lafiya inda ya tabbatar musu da adalci yayin hukunci kan wanda ake zargi

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kwamishinan 'yan sanda a jihar Kano, Hussaini Gumel ya umarci kama sifetan dan sanda kan zargin kisan matashi a Kano.

Gumel ya ba da umarnin ne ganin yadda dan sandan ya yi aiki ba tare da kwarewa ba wurin harbe matashin yayin zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Bidiyon zanga-zangar da ta barke a Kano kan zargin 'yan sanda sun kashe farar hula

'Yan sanda sun kama jami'ansu da ya hallaka matashi a Kano
An cafke dan sandan da ya hallaka matashi a Kano. Hoto: Haruna Kiyawa.
Asali: Facebook

Yaushe aka dauki mataki kan dan sandan a Kano?

Kakakin rundunar a jihar, Abdullahi Kiyawa shi ya tabbatar da haka a yau Laraba 29 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya kuma jawo raunata mutane da dama yayin da matasan ke zanga-zangar kan hukuncin kotun jihar da aka yanke.

Rundunar ta ce sifetan dan sandan bai samu wani umarni daga sama ba kan abin da ya aikata wanda ya yi ajalin matashin.

Kwamishinan ya kuma kafa kwamitin bincike don tabbatar da abin da ake ciki kan sifetan da kuma kisan kan, cewar TVC news.

Ya kuma umarci kwamnadan yankin Dala da ya jagoranci binciken don daukar matakin daya dace kan dan sandan.

Wane shawara 'yan sanda su ka bayar?

Gumel ya bukaci al'umma da su guji ta da zaune tsaye inda ya tabbatar musu da adalci yayin binciken da kuma hukunci.

Kara karanta wannan

Tsige Abba Gida Gida: An kama mutum 7 kan hukuncin Kotun Daukaka Kara, cikakken bayani

Jami'an sun cafke Sifetan dan sandan ne bayan ya harbe matashi mai suna Salisu Player a Unguwar Kurna da ke karamar hukumar Gwale a jihar.

Premium Times ta tattaro cewa matasan Unguwar sun fito zanga-zangar don nuna rashin jin dadinsu kan kisan matashin.

Gwamna Abba Kabir ya kawo dauki ga mahaukata

A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya umarci kwashe mahaukatan da ke yawo a titunan birnin Kano.

Gwamna ya dauki matakin ne bayan korafe-korafen jama'a kan yadda mahaukatan su ka cika birnin.

An kwashi mafi yawansu zuwa asibitin mahaukata don ba su kulawa na musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel