Kano: Mahaifiyar Wani Rikakken Dan Daba Ta Mika Shi Hannun Yan Sanda

Kano: Mahaifiyar Wani Rikakken Dan Daba Ta Mika Shi Hannun Yan Sanda

  • Ba kasafai ake samun irin hakan ba, mahaifiya ta dauki danta ta mika sa a hannun 'yan sanda don yana aikata laifi
  • A baya-bayan nan rundunar 'yan sanda ta ayyana dan daban da ake kira da Hantar Daba a matsayin wanda take nema ruwa a jallo
  • Mahaifiyar ta mika dan nata ne a ranar Litinin, inda kuma ta roki rundunar da ta sanya yaron nata a shirin gwamnati na yin afuwa don ya tuba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Mahaifiyar rikakken dan daba da ake nema ruwa a jallo a jihar Kano, ta yi ta-maza inda ta mika shi ga 'yan sandan jihar a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Yanzu: Tashin hankali yayin da jami'an NSCDC suka harbi dalibai a Abuja yayin jarrabawa

A baya-bayan nan ne rundunar 'yan sanda ta fitar da sanarwar sanya kyautar naira dubu dari biyar ga duk wanda ya gano inda dan dabar mai suna Hantar Daba ya ke.

Kwamishinan 'yan sanda/Mohammed Gumel/Jihar Kano
Mahaifiyarsa dan daban bayan mika sa hannun 'yan sanda, ta roki alfarmar a saka shi a shirin afuwa na gwamnatin jihar. Hoto: @KanoPoliceNG
Asali: Twitter

Ko me ya sa mahaifiyar ta mika danta ga 'yan sanda?

Kwamishinan 'yan sandan jihar Mohammed Gumel ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin rundunar, SP Haruna Abdullahi a ranar Talata, rahoton Tribuneonline.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Abin da ya faru a filin wasanni na Sani Abacha, Kofar Mata a ranar 17 ga watan Oktoba, 2023 ya canja tunanin mutane da dama.
"Mahaifiyar babban dan daban nan Hantar Daba ta rako danta tare da abokin adawarsa a baya amma yanzu amininsa Abba Burakita na Dorayi, yanzu suna hannun 'yan sanda."

Mahaifiyar Hantar Daba ta nemi ayi masa afuwa

Kara karanta wannan

Bidiyon zanga-zangar da ta barke a Kano kan zargin 'yan sanda sun kashe farar hula

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"Idan ba za ku manta ba, manyan 'yan daba uku da suka hada da Hantar Daba na kwanar Disu, Nasiru Abdullahi (Mai doki) na layin falwaya Kurna da Abba Burakita na Dorayi karama, sun addabi jihar Kano da aikin dabanci.
"Ko a wancan lokacin sai da rundunar 'yan sanda ta sanya kyautar naira dubu dari biyar akan duk wanda ya gano inda daya daga cikin matasan ya ke."

Legit ta ruwaito rundunar ta ce mutum na karshe a cikinsu, Hantar Daba wanda ake nemansa ruwa a jallo ya mika wuya ga rundunar a jiya Litinin, 27 ga watan Nuwamba, 2023.

"Mahaifiyarsa tare da rakiyar wasu 'yan uwansa suka mikasa ga 'yan sanda, tare rokon alfarmar a sanya shi a shirin afuwa na gwamnatin jihar."

Allah ya yi wa diyar Sarki Ado Bayero rasuwa

A safiyar yau ne Legit Hausa ta ruwaito maku cewa Allah ya yi wa diyar Sarkin Kano Ado Bayero rasuwa a safiyar ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba, 2023.

An gudanar da jana'izar Hajiya Hauwa Ado Bayero a gidan sarkin Kano, da misalin karfe goma na safiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel