Kano: Abba Kabir Ya Dauki Mataki Kan Mahaukatan da Ke Yawo a Titunan Birnin da Kewaye

Kano: Abba Kabir Ya Dauki Mataki Kan Mahaukatan da Ke Yawo a Titunan Birnin da Kewaye

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir ya ba da umarnin kwasar dukkan mahaukatan da ke yawo a tituna don kai su asibiti
  • Gwamnan ya ba da umarnin ne bayan samun korafe-korafe kan mahaukatan da ke yawo a titunan birnin musamman mata
  • Hadimar gwamnan a bangaren kula da marasa karfi da masu bukata ta musamman, Fauziyya Sulaiman ita ta bayyana haka a jiya Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Gamna Abba Kabir na jihar Kano ya umarci kwashe dukkan mahaukatan da ke jawo a tituna zuwa asibiti.

Gwamnan ya umarci kwashe mahaukatan ne da ke yawan yawo a cikin birnin Kano da ma kewaye don ba su kulawa na musamman a asibitocinsu.

Kara karanta wannan

An bankado sabon shirin tayar da hargitsi a jihar Kano kan hukuncin tsige Gwamna Abba

Abba ya kwashe mahaukata a kan tituna zuwa asibiti don kulawa da su
Abba Kabir ya dauki mataki kan mahaukatan da ke yawo a tituna. Hoto: @Kyusufabba.
Asali: Twitter

Wane umarnin Abba Kabir ya bayar a Kano?

Hadimar gwamnan a bangaren kula da marasa karfi da masu bukata ta musamman, Fauziyya Sulaiman ita ta bayyana haka a jiya Talata 28 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sulaiman ta bayyana haka ne a shafinta na Facebook inda ta ce an dauki matakin ne bayan samun korafe-korafe daga jama’a kan mahaukatan.

Ta koka kan yadda mafi yawan wadanda ake magana akansu mata ne wadanda ake zargin ana cin zarafinsu.

Wane martani hadimar gwamnan Kano ta yi?

Ta ce:

“Bayan samun korafi daga jama’a kan mahaukatan da ke yawo a kan tituna cewa mafi yawa mata na yawo tsirara wanda hakan ke jawo a ci musu zarafi.
“Gwamnan ya ba da umarnin kwashe su zuwa asibititocinsu don ba su kulawa ta musamman.”

Fauziyya ta kara da cewa sun fara wannan aiki karkashin jagorancin hukumar ba da agaji ta SEMA da kuma ofishinta.

Kara karanta wannan

Sheikh Bala Lau ya yabawa Uba Sani kan 'inganta walwalar' mazauna Kaduna

Ta ce akwai matar da tsawon shekaru ta na yawo tsirara sun saka likita ya mata allura kafin su ka iya daukarta zuwa asibiti, cewar Independent.

Abba Kabir ya nada sabon mukami

A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya nada sabon shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Alhaji Abdullahi Musa.

Wannan na zuwa ne bayan murabus din tsohon shugaban ma'aikatan Alhaji Usman Bala a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel