Bidiyon Zanga-Zangar da Ta Barke a Kano Kan Zargin ’Yan Sanda Sun Kashe Farar Hula

Bidiyon Zanga-Zangar da Ta Barke a Kano Kan Zargin ’Yan Sanda Sun Kashe Farar Hula

  • Al'ummar unguwar Kurna da ke birnin Kano sun fito zanga-zangar luma a safiyar ranar Laraba kan zargin 'yan sanda sun kashe wani matashi a unguwar
  • A daren ranar Talata rahotanni suka bayyana cewa wata hatsaniya ta tashi a unguwar Kurna, inda 'yan sanda suka kai dauki, sai dai abin ya zo da tangarda
  • Yayin da 'yan sanda ke kokarin kwantar da tarzomar, rahotanni sun nuna wani jami'i ya yi harbi da bindiga, inda ya samu fararen hula uku, Salisu ya mutu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kurna, jihar Kano - A daren jiya Talata ne muka samu rahoton wani rikici da ya faru tsakanin wasu da ake zargin 'yan daba ne da al'ummar wata unguwa da ke Kurna, birnin Kano.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama Babban Dan Siyasa, Wasu Kan Damfara Ta Naira Miliyan 607

Bayan bayyanar 'yan daban, masu shaguna suka rufe tare da neman tsira da rayuwarsu ganin yadda suke dauke da makamai, yayin da al'umma suka dau matakan kare kansu.

Zanga-zanga/Jihar Kano/Salisu Player
Sakamakon kashe wani matashi mai suna Salisu Player, al'ummar unguwar Kurna sun fito zanga-zangar lumana a Kano. Hoto: Mukhtar Kabir
Asali: Facebook

Me ya jawo kisan Salisu Player?

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Arewa Radio ta ruwaito cewa jami'an tsaro sun isa unguwar don kwantar da tarzoma, inda wani dan sanda ya fara harbi da bindiga lamarin da ya zama silar ajalin wani.

A rahoton gidan rediyon, harsashin bindiga ya samu wani matashi mai suna Alhaji Salisu Player, dan wasan kwallo a kungiyar kwallo ta Samba Kurna, inda ya mutu nan take.

Sai dai a safiyar ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, al'ummar unguwar Kurna suka fito zanga-zangar luma kan kashe dan unguwar da 'yan sandan suka yi.

Al'ummar unguwar Kurna sun fito zanga-zanga

Gidan rediyon Express da ke Kano, ya ruwaito cewa 'yan sandan sun harbi fararen hula uku ne a rikicin na daren jiya, sai dai Salisu Player ne ya mutu.

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram sun datse kawunnan mutane 11 masu sana’ar itace a Borno

Ya ruwaito cewa duk wani yunkuri na tuntubar 'yan sanda kan lamarin ya ci kuma, kuma har yanzu rundunar ba ta ce komai akai ba.

Legit ta ci karo da wallafar mutane da dama a kafar sada zumunta ta facebook, wadanda ke alhinin abin da ya faru ga matashin, inda da yawa ke rokon kwamishinan 'yan sandan jihar ya dau mataki.

Kalli bidiyon zanga-zangar:

Mahaifiyar rikakken dan daba a Kano ta mika shi hannun 'yan sanda

A wani labarin, mahaifiyar rikakken dan daba da ake nema ruwa a jallo a jihar Kano, ta yi ta-maza inda ta mika shi ga 'yan sandan jihar a ranar Talata, Legit Hausa ta ruwaito.

A baya-bayan nan ne rundunar 'yan sanda ta fitar da sanarwar sanya kyautar naira dubu dari biyar ga duk wanda ya gano inda dan dabar mai suna Hantar Daba ya ke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel