Jihar Kano
Sanusi Bature DawakinTofa ya sanar da cewa gwamnan Kano ya umarci kwamishinonin da aka canza su shiga ofis tsakanin Litinin zuwa ranar Laraba za a ga sauyi.
Ibrahim Mukhtar ba zai hakura da ruguza gininsa da jami’an KNUPDA suka yi a jihar Kano ba Yake cewa sun wayi gari ne kurum, sai suka ji labarin an kai ginin kasa.
Bayan kiran Sarki Muhammadu Sanusi II da tsohon sarki, Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah ya nemi afuwar al'umma musamman masoyansa kan kalaman da ya yi.
Sanata Barau Jibrin ya yi godiya ga manyan mutane da suka halarci daurin auren 'ya'yansa da na sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero a masallacin kasa na Abuja.
Babbar kotun jihar Kano ta haramtawa jami'an tsaro shirin kama hadimin Gwamna Abba Kabir a bangaren sadarwa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa kan zargin Abdullahi Ganduje.
Adnan Mukhtar Adam Tudunwada bai ganin rashin lafiya ta sa aka kori Abdullahi Baffa Bichi, a nan ya jero dalilan tankade da rairaya a gwamnatin Kano.
Hukumar kwana-kwana ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar ma'aurata sakamakon wata gobara da ta afku a yankin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano.
Jarumai mata da maza sun cika wajen bikin diyar Asma'u Sani, suna wasa, dariya, da daukar hotuna a ranar daura aure, wanda ya kayatar kwarai da gaske.
Kungiyar Arewa ta shawarci gwamnati a kan kudirin haraji. Kakakin kungiyar reshen Kano, Bello Sani Galadanchi ne ya shaida wa lamarin a ranar Juma'a.
Jihar Kano
Samu kari