Ana Murnar Ramadan, An Kama Shugaban Ƙaramar Hukuma da Zargin Sata a Kano

Ana Murnar Ramadan, An Kama Shugaban Ƙaramar Hukuma da Zargin Sata a Kano

  • Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Kano watau PCACC ta kama shugaban ƙaramar hukumar Kiru, Hon. Abdullahi Mohammed
  • Mai magana da yawun PCACC, Kabir Abba Kabir ya tabbatar da lamarin, ya ce an tsare shi ne kan sayar da wani fili da za a gina filin wasa
  • Bincike ya nuna hukumar ta gano kamfanin da ya sayi filin kuma ya tura kudin zuwa asusun kai da kai na shugaban ƙaramar hukumar Kiru

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Hukumar karɓar korafe-korafe da yaki da cin hanci ta jihar Kano (PCACC) ta kama shugaban ƙaramar hukumar Kiru, Abdullahi Mohammed.

Hukumar PCACC ta cafke ciyaman din ne bisa zargin sayar da fili da aka ware don gina filin wasa na 'Kafin Maiyaki Mini Stadium'.

Muhuyi Magaji Rimin Gado.
An kama shugaban karamar hukumar Kiru a Kano kan zargin cin hanci Hoto: Muhuyi Magaji Rimin Gado
Asali: Facebook

PCACC ta cafke shugaban karamar hukuma

Kara karanta wannan

Zanga zanga: 'Yan Najeriya za su yi tirjiya ga Tinubu kan karin kudin wuta

Daily Trust ta ce binciken da hukumar ta gudanar ya gano cewa wani kamfani mai suna Mahasum ya sayi wadannan filayen da aka tanada don filin wasa kan kudi fiye da Naira miliyan 100.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kuma hukumar ta gano cewa kamfanin ya tura kudaden kai tsaye zuwa asusun ajiyar Abdullahi Mohammed ba tare da bin ka’idojin gwamnati ba.

A cewar mai magana da yawun hukumar, Kabir Abba Kabir, an tabbatar da cewa daga 1 ga Nuwamba, 2024, zuwa 27 ga Fabrairu, 2025, an zuba aƙalla Naira miliyan 240 a cikin asusun ajiyar ciyaman ɗin Kiru.

Wannan adadin ya haifar da tambayoyi masu yawa, wanda hakan yasa hukumar ta gaggauta daukar matakin kama shi domin gudanar da bincike mai zurfi.

An kwato kudi daga hannun ciyaman

Hukumar ta ce ta samu nasarar kwato dukkan wadannan kudade da aka biya, domin tabbatar da an mayar da dukiyar al'umma inda ya dace.

Kara karanta wannan

Kotu ta ba da belin Farfesa Usman Yusuf, ta gindaya masa sharuda

Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban ƙaramar hukumar na bada hadin kai ga jami’an bincike yayin da suke kokarin bankado duk wanda ke da hannu a wannan badakala.

Wannan mataki ya janyo cece-kuce a tsakanin al’ummar jihar Kano, musamman mutanen yankin Kiru da ke ganin cewa wannan lamarin na iya hana su samun ci gaba.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana bacin ransu, suka bukaci gwamnatin jihar da ta dauki matakan da suka dace domin tabbatar da an hukunta duk wanda ke da hannu a wannan badakala.

Abba da Muhuyi.
Hukumar PCACC ta ce ba wanda za ta ɗaga wa kafa matukar aka gano yana da laifi Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Babu wanda hukuma za ta ɗagawa kafa

A hannu guda kuma, hukumar PCACC ta jaddada kwarin gwiwa cewa za ta ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa, tare da tabbatar da gaskiya da adalci a shugabanci.

Hukumar ta ce babu wanda za ta ɗaga wa ƙafa matukar an same shi da aikata laifin almundahana da dukiyar al’umma, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ɓullo da sabuwar dabara, mataimakin ciyaman ya faɗa tarko a Zamfara

A karshe, hukumar ta bukaci Kanawa da su ci gaba da bai wa hukumomi hadin kai, tare da kai korafi idan suka ga wata badakala domin a dauki matakin da ya dace.

An dakatar da shugaban ma'aikatan Kano

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Kano ya dakatar da mukaddashin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Salisu Mustapha kan zargin zabtare abashin ma'aikata.

Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ya ɗaga wa kowa ƙafa ba, duk da wanda aka kama da hannu a zaftarewa ma'aikata albashi zai fuskanci hukunci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262