2027: Barau na Barazana ga Siyasar Abba, Ya Cigaba da Wawushe Mawakan Kwankwasiyya
- Fitattun mawakan Kannywood, Sadiq Zazzabi da Shalelen Mawaka, sun fice daga tafiyar Kwankwasiyya zuwa APC
- Mawakan sun bayyana sauya shekarsu a gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin a Abuja
- A lokacin karbarsu, Barau ya yi alkawarin ci gaba da tallafawa masana'antar Kannywood da matasa baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - A wani mataki da ya jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasa da masana'antar Kannywood, fitattun mawaka sun sauya sheka.
Mawakan Kannywood, Sadiq Zazzabi da Abdulmuminu Muhammad, wanda aka fi sani da Shalelen Mawaka, sun sauya sheka daga tafiyar Kwankwasiyya zuwa jam’iyyar APC.

Asali: Facebook
Sanata Barau Jibrin ne ya tabbatar da matakin da mawakan suka dauka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta tattaro cewa mawakan sun dauki matakin ne a gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da ke Abuja.
Sun bayyana cewa goyon bayan da Sanata Barau ke bai wa masana'antar Kannywood ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkokin su.
Mawakan Kwankwasiyya sun koma APC
A yayin da yake bayani, Sadiq Zazzabi ya ce goyon bayan da Sanata Barau ke bai wa masana’antar Kannywood ne ya sa suka yanke shawarar barin Kwankwasiyya.
Mawakin ya ce:
"Goyon bayan Sanata Barau ya inganta harkokinmu, har ya sanya muna iya yin gogayya da takwarorinmu daga kudancin kasar nan."
A nasa bangaren, Shalelen Mawaka ya ce sun yanke shawarar sauya sheka ne domin samun ci gaba da kuma karin damammaki a karkashin APC.
Sanata Barau ya karbe su hannu bibbiyu
Sanata Barau Jibrin ya bayyana farin cikinsa da shigowar wadannan fitattun mawakan Kannywood a cikin jam'iyyar APC.
A cewarsa:
"Jam’iyyar APC gida ne da zai karbi kowa. Mun bude hannu don maraba da ku, kuma za a muku cikakken adalci kamar kowane dan jam’iyya."
Har ila yau, ya yi alkawarin ci gaba da tallafawa masana’antar Kannywood, yana mai cewa masana’antar tana taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi ga matasa.

Asali: Facebook
Tasirin sauya-shekar ga harkokin Kannywood
Sauya sheka da wadannan mawaka suka yi zai iya yin tasiri a siyasar masana’antar Kannywood, wadda ke da dimbin magoya baya a Arewacin Najeriya.
Masana harkokin siyasa na ganin matakin na iya kara karfafa APC a tsakanin masu ruwa da tsaki a masana’antar fim da waka.
A gefe guda, masu goyon bayan Kwankwasiyya na iya kallon sauya shekar mawakan a matsayin koma baya ga tafiyar su, musamman duba da rawar da suka taka a yakin neman zaben NNPP.
A daya bangaren kuma, wasu 'yan Kwankwasiyya za su iya ganin sauya shekar ba a bakin komai ba kasancewar su ma suna karbar 'yan wata jam'iyya zuwa NNPP.

Kara karanta wannan
Tsohon shugaba Buhari, El-Rufa'i da sauran jagororin APC sun ki halartar taron APC
Mawakin Kwankwasiyya ya koma APC
A wani rahoton, kun ji cewa wani mawakin Kwankwasiyya, Abubakar Sani Dan Hausa ya koma jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Abubakar Sani Dan Hausa ya sauya sheka ne a gidan Sanata Barau Jibrin da ke birnin tarayya Abuja bisa wasu dalilai da ya ambata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng