Jihar Imo
Hukumar zaɓe ta INEC ta fitar da jerin sunayen ƙarshe na ƴan takarar gwamna a jihohin Kogi, Bayelsa da Imo. Zaɓen gwamna a jihohin zai gudana a watan Nuwamba
Kungiyar gwamnonin APC ta zabi gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma a matsayin shugabanta inda zai gaji tsohon gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Atiku Bagudu.
Ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani babban faston ɗariƙar Katolika a jihar Imo. Ƴan bindigan sun kwamushe Rev Fr Michael Opara ne yana kan hanyar dawowa gida.
Yan bindiga sun hallaka wani mai sarautar gargajiya na Orsu Obota Eze Victor Ijioma a karamar hukumar Oguta da ke jihar Imo, kuma suka kona gawarsa a cikin mota
Ɗan majalisar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Imo, Hon. Jerry Alagbaoso, ya fice daga jam'iyyar zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Ƴan bindiga sun kai mummunan farmaki kan jami'an ƴan sanda a ƙaramar hukumar Ngor Okpala ta jihar Imo. A yayin farmakin an samu asarar rayukan ƴan sanda biyu.
'Yan bindiga sun je har gida sun sace shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a ƙauyen Umuarugo, cikin ƙaramar hukumar Ehime Mbaino a jihar Imo.
Wasu 'yan bindiga sun hallaka Kyaftin Tony Enoch wanda jigo ne a jam’iyya mai mulki ta APC, kuma amini ga gwamnan jihar da zababben shugaban kasa Bola Tinubu.
Gwamna Ademola Adeleke da wasu gwamnoni 4 da suka yi nasara a kotu bayan shafe watanni ana dambarwa a kotuna daban daban sakamakon zabubbuka da aka gudanar.
Jihar Imo
Samu kari