Gwamna Inuwa, Danwambo Sun Hadu a Jana'iza Kasa da Wata 3 kafin Gwada Kwanji a Zabe
- Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa sallar jana’izar Nasiru Dankwambo, ƙanin tsohon gwamna Ibrahim Dankwambo
- Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga Sanata Ibrahim Dankwambo da iyalansa, yana mai bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga iyali da Gombe baki ɗaya
- Hakan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zabe mai zafi tsakanin Gwamna Inuwa da Sanata Dankwambo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Ana hasashen zaben jihar Gombe na daga cikin waɗanda za su yi zafi tsakanin APC, PDP da ADC.
Sai dai gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya yi abin a yaba bayan ziyarar ta'aziyya ga abokin hamayyarsa, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo.

Source: Facebook
Sakataren yada labaran gwamnan Gombe, Ismaila Uba Misilli shi ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook.
Inuwa ya hadu da Dankwambo a jana'iza
An yaba wa gwamnan bisa wannan karamci da ya nuna duk da shirin fafatawa da suke yi da Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo.
Inuwa ne ya kwace mulki a hannun PDP bayan kammala wa'adin Ibrahim Hassan Dankwambo na shekaru takwas.
Daga bisani Dankwambo ya yi nasarar tafiya majalisar dattawa a 2019 har zuwa yanzu da ya ke neman wa'adi na biyu.
Ana ganin zaɓen zai yi zafi saboda neman sanatan Gombe ta Arewa da Inuwa da Dankwambo ke yi.
Dankwambo shi ne jagoran PDP a Gombe da ta ba Isa Ali Pantami takara domin fafatawa da Jamilu Isiyaku Gwamna a APC.
Sai dai INEC ta cire sunansa a jerin sunayen wadanda za su yi takarar gwamna da na majalisar dokokin jihohi a zaɓen 2026.
Bayan korafe-korafe, INEC ta ba masu adawa da hakan zuwa ranar 24 ga watan Oktoba domin daukar matakin karshe.

Kara karanta wannan
Lokacin tafiya ya yi: Tsohon gwamna a Najeriya ya rasu yana da shekaru 71 a duniya

Source: Facebook
Gwamna Inuwa ya ziyarci jana'izar kanin Dankwambo
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa sallar jana’izar Nasiru Dankwambo, ƙanin tsohon gwamna kuma Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo.
Marigayin ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Litinin, lamarin da ya jefa iyalansa da sauran makusantansa cikin alhini da jimami.
An gudanar da sallar jana’izar ne a masallacin da ke asibitin koyarwa na tarayya, Federal Teaching Hospital, da ke Gombe, inda Sheikh Muhammadu Adamu Dokoro ya jagoranci sallar.
Bayan kammala sallar, Gwamna Inuwa Yahaya ya miƙa ta’aziyyarsa ga Sanata Dankwambo da sauran ’yan gidan mamacin, yana bayyana alhininsa kan wannan babban rashi.
Tun da farko, gwamnan ya fitar da saƙon ta’aziyya a hukumance ga magabacinsa, inda ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi da lokacin alhini ga iyalan Dankwambo da jihar Gombe baki ɗaya.
Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa mamacin kura-kuransa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdausi, sannan Ya ba iyalansa haƙuri da ƙarfin zuciyar jure wannan babban rashi.
Dankwambo ya shiga kamfen Tinubu
Kun ji cewa APC ta fitar da sabon jerin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda aka haɗa Nyesom Wike, da gwamnonin adawa.
Bola Tinubu zai jagoranci kwamitin, yayin da Kashim Shettima da Nentawe Yilwatda za su kasance mataimakan shugabanni, tare da Godswill Akpabio.
APC ta naɗa Abdulaziz Yari darakta janar, yayin da Hope Uzodimma zai zama sakatare, domin tsara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Asali: Legit.ng

