Asiri Ya Tonu: An Gano Masu Shirya Kai Farmaki kan Matasan da Za Su Yi Aikin Zaben 2027
- Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce DSS ta gano waɗanda ake zargi da hannu a shirin kai w# wadanda za su yi aikin zabe hari
- Hukumar ta bayyana cewa ta ɗauki matakan kare ma’aikatanta na wucin gadi, musamman mambobin NYSC, daga barazanar tsaro
- Amupitan ya yi gargaɗi kan yaɗa labaran ƙarya, rashin amincewar jama’a da rashin zuwa kaɗa ƙuri’a a lokacin babban zabs
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar DSS ta gano tare da kama waɗanda ake zargi da shirya kai wa ma’aikatan wucin gadi na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) hari a zaben 2027.
An ruwaito cewa wadanda ake zargin sun shirya kai harin ne musamman kan matasa Masu Yi Wa Ƙasa Hidima (NYSC), gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a Enugu yayin taron tattaunawa da ma’aikatan hukumar na shiyyar Kudu maso Gabas.
A cewar sanarwar da hukumar ta fitar, INEC ta gano yiwuwar barazanar da ka iya shafar tsaron ma’aikatanta na wucin gadi, musamman masu yi wa ƙasa hidima, kuma ta ɗauki matakan rage haɗarin.
Amupitan ya ce DSS ta gano waɗanda ake zargi da hannu a shirin, inda ya ƙara da cewa nan ba da daɗewa ba za a gurfanar da su a gaban kotu.
Hukumar INEC za ta shirya taron tsaro
Shugaban INEC ya kuma sanar da shirin shirya taron tsaro domin tattauna sababbin matsalolin da suka shafi tsaron zaɓe.
Ya ce hukumar ta ƙarfafa haɗin gwiwarta da Kwamitin Haɗin Gwiwa na Hukumomin Tsaro kan Tsaàron Zaɓe (ICCES), sannan tana aiki tare da hukumomin tsaro na ƙasa da na jihohi domin inganta shirye-shiryen zaɓen.
A cewarsa, INEC na amfani da kayan aikin Gudanar da Haɗarin Zaɓe (ERM) domin samar da ingantaccen tsarin tsaro da ya dogara da bayanan sirri.

Kara karanta wannan
2027: Shugaban INEC ya sanar da ma'aikatan hukumar abin da ba za su yarda da shi ba
Barazanar labaran ƙarya ga zabe
Amupitan ya bayyana rashin amincewar jama’a, rashin sha’awar masu kaɗa ƙuri’a da kuma yaɗuwar bayanan ƙarya a matsayin manyan ƙalubalen da hukumar ke fuskanta.
Ya yi gargaɗin cewa labaran ƙarya, jita-jitar da ba a tantance ba da kuma bidiyoyin bogi da aka ƙirƙira ta amfani da fasahar zamani na iya yaɗuwa cikin sauri a shafukan intanet, lamarin da zai iya raunana amincewar jama’a da tsarin zaɓe.

Source: Twitter
Shugaban INEC ya ce hukumar za ta tunkari waɗannan ƙalubale ta hanyar gaskiya da buɗaɗɗen aiki, bayar da sahihan bayanai cikin gaggawa da kuma bin ƙa’idojin gudanar da ayyuka a rumfunan zaɓe.
INEC ta gargadi ma'aikatanta
Kun ji cewa shugaban INEC ya gargaɗi ma’aikatan hukumar da su guji nuna goyon baya ga kowace jam’iyyar siyasa, su kuma kasance masu adalci da ƙwarewa.
Hukumar ta bullo da tsarin lada da hukunci domin ƙarfafa ladabtarwa da ɗaukar alhaki a ofisoshinta na ƙananan hukumomi, jihohi da ƙasa baki ɗaya.
Asali: Legit.ng
