Wata Tsohuwa Mai Shekaru 95 Ba Aure Ta Bayyana Yadda Mahaifinta Ya Jawo Mata, An Yada Bidiyon

Wata Tsohuwa Mai Shekaru 95 Ba Aure Ta Bayyana Yadda Mahaifinta Ya Jawo Mata, An Yada Bidiyon

  • Faifan bidiyon wata mata ‘yar shekaru 95 da ba ta taba aure ba a garin Emekuku da ke jihar Imo ya girgiza mutane
  • Duk da yawan manema da ta ke da su a wancan lokaci, amma ba ta samu ta yi aure ba saboda bambancin akida na Kiristanci
  • Mutane sun yi martani bayan ganin wannan bidiyo mai ban tausayi, inda su ka ce mahaifin bai kyauta mata ba

An wallafa wani faifan bidiyo mai taba zuciya ga duk wani mai tausayi inda wata tsohuwa ta bayyana yadda ta tsufa babu miji.

Wata budurwa mai suna @nelojosh ita ta wallafa bidiyon a TikTok na wata tsohuwa mai shekaru 95 daga garin Emekuku da ke jihar Imo, Legit ta tattaro.

Tsohuwa 'yar shekara 95 ta bayyana dalilin rashin yin aure a faifan bidiyo
Tsohuwa Mai Shekaru 95 Ta Bayyana Dalilin Rashin Yin Aure A Rayuwarta. Hoto: @nelojosh/TikTok.
Asali: TikTok

Meye faifan bidiyon ke dauke da shi?

Kara karanta wannan

Rahama Sadau Ta Fayyace Dalilin Da Ya Sa Take Jawo Cece-Kuce, Ta Ce Ba Da Nufi Ba Ne

A cikin faifan bidiyon, tsohuwar ta bayyana yadda ta zauna babu aure har lokacin tsufarta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce laifin mahaifinta ne saboda ya ki duk wadanda su ke zuwa nemanta saboda ba su fito daga akidar Katolika ba na Kiristanci.

Duk yawan manema da ta ke da su amma mahaifin nata ya ce dole sai wanda ya ke Katolika.

Ta ce:

“Ina da manema da dama amma mahaifina har kiran Fasto ya ke ya fahimtar da ni auren wanda ba ya akidar da ya ke so.”

Ku kalli bidiyon a kasa:

Tsohuwar wacce har zuwa yanzu ba ta rude ba, ta bayyana cewa kannenta duka sun samu mazan aure duka daga akidar Katolika.

Wannan faifan bidiyo ya jawo martanin mutane musamman wadanda su ka nuna tausayawa kan lamarin da ya faru da ita.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wata Mata Ta Faɗi Ta Mutu a Kan Gada Cikin Yanayi Mai Ban Tausayi

Meye Martanin mutane kan faifan bidiyon?

Jama’a da dama sun yabi yadda ta ke magana kanta daya duk da tarun shekarunta a duniya har 95.

@Urhobo babe:

“Allah wadaran wannan mahaifin nata.”

@onvinwokikebuchai:

“Har yanzu ta na da kwakwalwa duk da shekaru 95, wannan abin burgewa ne.”

@Chidinma Deb:

“Ko ba komai ta yi tsawon rai.”

@lilianibechukwu:

“Kun ga irin bin akidar ta jefa ta ko saboda mahaifinta,”

@SharonofEnugu:

“Na dade da fadawa iyayena cocin da mutum ke zuwa ba zai hana ni auren masoyi na ba.”

@Olayinka:

“Mahaifin nan bai kyauta mata ba ko kadan.”

@ugochinyereofoefu:

“Na so ace mahaifin na nan yanzu ya ga yadda lamura su ke.”

Budurwa ta fadi kyautar da saurayinta ya ba ta a shekaru 11

A wani labarin, wata budurwa ta wallafa wani bidiyo yayin da ta ke zayyana abubuwan da saurayinta ya siya mata tsawon shekaru 11 da su ka yi su na yi.

Kara karanta wannan

Abin Tausayi Yayin Da Uwa Ta Kona Dan Cikinta Da Ruwan Zafi Kan Zargin Neman Mata, Bayanai Sun Fito

Budurwar ta bayyana cewa tuni ta mayar masa da abubuwa ukun da ya taba siya mata da su ka hada da buroshin goge hakora da safa da kuma man kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel