Yan Bindiga Sun Halaka Sojoji Takwas da 'Yan Sanda a Jihar Imo

Yan Bindiga Sun Halaka Sojoji Takwas da 'Yan Sanda a Jihar Imo

  • Yan bindiga sun yi wa tawagar jami'an Soji, 'Yan sanda da Sibil defens kwantan ɓauna, sun halaka aƙalla 8 a jihar Imo
  • Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa maharan sun ƙone jami'an tsaron har lahira a cikin motoci guda biyu
  • Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce zata tattara bayanai ƙafin fitar da sanarwa a hukumance

Jihar Imo - Wasu 'yan bindiga sun kashe akalla jami'an tsaro Takwas da suka ƙunshi sojoji, 'yan sanda da jami'an Sibil Defens a jihar Imo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Jaridar Punch ta tattaro cewa mummunan lamarin ya auku ne da safiyar Talata (yau) 19 ga watan Satumba, 2023 a yankin Umualumaku, karamar hukumar Ehime Mbano.

Harin yan bindiga a jihar Imo.
Yan Bindiga Sun Halaka Sojoji Takwas da 'Yan Sanda a Jihar Imo Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Kisan jami'an tsaron ya haddasa tashin hankali da firgici a zuƙatan mutanen da ke rayuwa a yankin.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Bindiga Sun Halaka Mutane da Yawa a Garuruwa 7 Na Jihohin Arewa 2, Sun Tafka Ɓarna

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun ɗana wa jami'an tsaron haɗin guiwar tarko, kana suka banka wa motocinsu biyu wuta kuma duk suna ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babu wanda ya tsira daga cikin jami'an tsaron da ke cikin motocin saboda maharan sun ƙone su ne ba tare sun bari sun fito daga motocin ba.

Wane mataki jami'an tsaron suka ɗauka?

Wani jami'an tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa jaridar The Nation cewa tuni aka tura ƙarin dakarun tsaro da nufin damƙe yan ta'addan da kuma kwaso gawar mamatan.

Wani mazaunin yankin da bai so ya bayyana sunan sa saboda dalilan tsaro ya ce ya ga jami’an tsaron da idonsa ‘yan mintoci kadan kafin a kona su.

Ya bayyana cewa kashe sojojin da ƴan sanda ya jefa ɗaukacin mazauna yankin cikin ruɗani, tashin hankali da fargaba, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Direban Babbar Mota Ya Murkushe Jami'in Hukumar FRSC Har Lahira, Bidiyo Ya Bayyana

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya nemi a ba shi lokaci domin samun cikakken bayani kan wannan mumunan hari.

Manoma da Dama Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Kai Hari Kauyuka 7 a Kebbi da Sokoto

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun yi ajalin rayukan manoma da yawa yayin sabon harin da suka kai ƙauyukan bodar jihohin Kebbi da Sakkwato.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun tarwatsa kauyuka 7, bisa tilas mutane suka gudu daga gidajensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel