"Babu Zagi": Yari Ya Fadi da Abin da Za Su Tallata Shugaba Tinubu da Shi
- Jam’iyyar APC ta ce za ta gudanar da kamfen cikin mutunci, ba tare da zagi ko kai hare-hare na kashin kai kan ’yan adawa ba
- APC mai mulki na neman ’yan Najeriya su sake zaɓar Tinubu domin ya ci gaba da mulki a wa’adi na biyu
- An tsara ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a hukumance a Jihar Kaduna ranar Asabar, 24 ga Oktoba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta mayar da hankali kan ayyukan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gudanar a yaƙin neman zaɓen 2027, maimakon yin zagi ko kai hare-hare na kashin kai kan ’yan takarar jam’iyyun adawa.
Yari ya ce jam’iyyar za ta gudanar da kamfen cikin mutunci, bisa muhimman batutuwan da suka shafi ƙasa, inda za ta gabatar wa ’yan Najeriya ayyukan da ta gudanar a matsayin hujjar neman wa Tinubu wa’adi na biyu.

Source: Facebook
Abdulaziz Yari ya gana da Bola Tinubu
Jaridar Leadership ta ce ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 20 ga watan Oktoban 2026 a Abuja, bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu tare da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.
Sun gana ne domin yi wa shugaban ƙasa bayani kan shirye-shiryen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar a hukumance.
A cewar Yari, kwamitin yaƙin neman zaɓen ya yanke shawarar mayar da hankali kan ayyukan da gwamnatin Tinubu ta gudanar da manufofinta, maimakon shiga zagin mutane ko kai musu hare-hare na kashin kai.
Da me APC za ta tallata Tinubu?
"A matsayarmu na kwamiti, mun bayyana abin da za mu yi. Za mu gudanar da kamfen bisa ayyukan da muka yi. Kamfen na mutunci, babu zagi ko kiran mutane da sunayen batanci, domin ba sunaye ne a gabanmu ba, sai dai ayyukan da za mu nuna wa ’yan Najeriya.” In ji shi.
Tsohon gwamnan Jihar Zamfara ya bayyana cewa APC za ta yi amfani da kamfen ɗin wajen bayyana manufofi da shirye-shiryen da gwamnatin Tinubu ta aiwatar, tare da roƙon ’yan Najeriya su yi la’akari da ayyukan gwamnatin kafin su yanke shawarar ko za su sake ba ta damar ci gaba da mulki.
“Wannan shi ne abin da jam’iyyarmu ta yi, wannan shi ne abin da gwamnatinmu ta aiwatar. Saboda haka, muna roƙon ’yan Najeriya da su duba waɗannan ayyuka da kyau, domin su sake ba mu dama ta biyu don ci gaba da ayyukan.” In ji shi.
APC na shirye-shiryen zaben 2027
Jawabin Yari ya zo ne a daidai lokacin da APC ke ƙara tsananta shirye-shiryen gudanar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a faɗin ƙasar gabanin babban zaɓen 2027.
Jihar Kaduna ce aka tsara za ta karɓi baƙuncin ƙaddamar da kamfen ɗin shugaban ƙasa na jam’iyyar a hukumance a ranar Asabar, 24 ga Oktoba.

Source: Facebook
Dalilin su Yari na zuwa wajen sarakuna
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Abdulaziz Yari, ya ce ziyarar da su ke kai wa sarakunan gargajiya ba ta da manufar neman amincewar siyasa.
Sanata Yari, tsohon gwamnan Zamfara, ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce neman addu’a, albarka da shawarwari masu amfani daga sarakunan gargajiya.
Asali: Legit.ng

