Wahalar man fetur a Najeriya
Ana tsaka da tsadar man fetur a Najeriya, Shugaba Tinubu ya tura wa shugaban NNPC sako a ranar Litinin. Tinubu ya taya Mele Kyari murnar cika shekaru 59.
A kan kusan N700, kasashe 21 kacal su ka fi Najeriya arahar farashin fetur. Mun tattaro farashin da ake sayen litar man fetur a gidajen mai a kasashen duniya.
Kamfanin mai na ƙasa NNPCL da yan kasuwa sun amince da cewa ba zancen ƙarin farashin litar man fetur a Najeriya nan da yan kwanaki, farashi na nan daram.
Kungiyar kare hakkin dan Adam da wayar da kan jama'a, CHRICED ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya biye wa Bankin Duniya wurin kara farashin mai da wutar lantarki.
Kungiyar TUC ta sake tura sabbin bukatu 10 ga Shugaba Bola Tinubu yayin da aka shiga sabuwar shekara inda ta ce dole ya aiwatar da su ko ya fuskanci matsala.
Yayin jita-jita ta fara yawaita kan yunkurin kara farashin litar man fetur, Gwamnatin tarayyan Najeriya ta musanta batun, kana ta kwantarwa yan Najeriya da hankali.
An yi kira ga jama'a da su kauracewa yawan tu'ammali da man fetur, barasa da sigari da kuma magungunan kashe kwari don kaucewa kamu da cutar sankarar bargo.
Kamfanin NNPCL wanda shi ne ke kula da harkar mai a Najeriya ya ce farashin fetur bai koma N1, 200 a yanzu ba, ya jaddada cewa an yi waje da tallafin fetur.
Kamfanin mai na kasa wanda aka fi sani da NNPCL yace babu tallafi amma har yanzu ana sayen man fetur ne a kan N617-N690, duk da ikirarin cire tallafi tun 2023
Wahalar man fetur a Najeriya
Samu kari