Matatar Man Dangote Ta Bayyana Ranar Fara Aiki Bayan Ta Kasa Farawa a Watan Agusta

Matatar Man Dangote Ta Bayyana Ranar Fara Aiki Bayan Ta Kasa Farawa a Watan Agusta

  • Wani sabon rahoto ya bayyana cewa matatar man Dangote ta sanya sabuwar ranar da za ta fara aiki bayan ta kasa farawa a lokacin farko da ta sanya
  • A watan Agustan 2023 ne aka sa ran fara aikin matatar man fetur ɗin da ke a Legas bayan da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da ita
  • Matatar man fetur ɗin za ta riƙa samar da gangar man fetur 650,000 a kowace rana, wanda hakan zai magance ƙalubalen shigo da mai zuwa Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Matatar man fetur ɗin Dangote ta sanar da cewa za ta fara aikin tace ɗanyen man fetur a watan Oktoban 2023. Babban Daraktan rukunin kamfanonin Dangote, Devakumar Edwin, wanda ke kula da aikin, shi ne ya bayyana hakan.

Edwin ya gayawa S&P Global Commodity Insights cewa matatar tana sa ran isowar jirgin ɗanyen man fetur ɗinta na farko nan da sati biyu, inda za a fara aiki bayan isowarsa.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Hari Jihar Arewa, Sun Sace Mahaifi Tare Da Diyarsa

Matatar man Dangote za ta fara aiki a Oktoba
Matatar man Dangote ta shirya fara aiki a watan Oktoba Hoto: Ankomah / Contributor
Asali: Getty Images

Ya yi bayanin cewa za a fara fitar da ganga 370,000 a kowace rana na man dizal da man jirgin sama a watan Oktoba, sannan za a fara tace man fetur a watan Nuwamban 2023.

"A shirye muke mu karɓi ɗanyen man fetur a yanzu. Muna jiran isowar jirgin farko ne, kuma da zarar ya iso, za mu iya fara aiki." A cewarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aikin matatar man Dangote

Matatar dangote na da ƙarfin tace gangar man fetur 650,000 a kowacce rana, kuma da yawa daga cikin ƴan Najeriya ciki har da gwamnatin tarayya na fatan za ta kawo ƙarshen dogaron da ƙasar ke yi na shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje.

Masana sun kuma sun yi nuni da cewa cewa matatar man tana da damar sanya Najeriya a matsayin mai fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje musamman ƙasashen Afirka.

Kara karanta wannan

Rayuka Da Dama Sun Salwanta Bayan Wasu Motoci Sun Yi Taho Mu Gama

Sai dai, an sha shakku kan matatar a cikin ƴan watannin nan saboda jinkirin da aka samu wajen fara aikinta da saɓa lokacin da aka ce za ta fara aiki.

A ranar 22 ga Mayu, 2023, lokacin da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da ita, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya yi alkawarin cewa matatar man za ta fara aiki a ƙarshen watan Yuli ko farkon watan Agusta.

Dangote Ya Fita Daga Jerin Attajirai 100 Na Duniya

A wani labarin kuma, attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aliko Dangote ya rikito daga cikin jerin attajaran duniya 100.

Hamshakin attajirin wanda babu wanda ya kai shi kuɗi a nahiyar Afirika, ya fita daga cikin jerin ne bayan ya tafka asarar N36bn a cikin sa'o'i kaɗan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel