NNPC Na Bin Tinubu Bashin Naira Tiriliyan 7.3 Na Tallafin Mai Bayan Faduwar Darajar Naira

NNPC Na Bin Tinubu Bashin Naira Tiriliyan 7.3 Na Tallafin Mai Bayan Faduwar Darajar Naira

  • Yayin da aka dawo da tallafin mai a Najeriya, rikita-rikita ta barke kan basukan da NNPC ke bin Gwamnatin Tarayya
  • NNPC ta ce a yanzu haka ta na bin Gwamantin Tarayya makudan kudade har Naira tiriliyan 7.3 na tallafin mai a kasar
  • Kafin cire tallafin mai da Shugaba Tinubu ya yi, NNPC na kashe Naira biliyan 400 a ko wane wata don shigo da mai

FCT, Abuja Kamfanin mai na NNPC ya bayyana cewa ya na bin Gwamnatin Tarayya bashi Naira tiriliyan 7.3 na tallafin mai.

Kamfanin ya ce gwamnatin ta rike Naira tiriliyan 4.1 inda ta kuma ta gaza tura Naira tiriliyan 2.8 zuwa ga asusun Gwamnatin Tarayya yayin da ta kuma rike wa kamfanin Naira tiriliyan 1.3.

NNPC na bin FG bashin Naira tiriliyan 7 na kudin tallafi
Kamfanin NNPC Na Bin Gwamnatin Tinubu Bashin Naira Tiriliyan 7.3. Hoto: Anadolu Agency/Contributor.
Asali: Getty Images

Meye ya jawo bashin da NNPC ke bin Tinubu?

Kara karanta wannan

Dangote Ya Dare Mataki Na 1 A Jerin Mafi Tafka Asara A Nahiyar Afirka, An Bayyana Yawan Asarar Da Ya Yi

Kafin cire tallafin mai a watan Mayu da Shugaba Tinubu ya yi, NNPC na kashe Naira biliyan 400 a ko wane wata don shigo da man fetur kasar, Legit ta tattaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga watan Janairu zuwa Mayu na 2023 biyan kudin ya karu da kaso 55 idan aka kwatanta da shekarar bara.

Daily Trust ta tattaro cewa NNPC ya samu sako daga asusun Gwamnatin Tarayya na biyan Naira tiriliyan 2.8 na bashin da kamfanin ke bin gwamnatin.

Har ila yau, kamfanin ya ce ba zai biya kudaden ba idan har gwamnatin ta biya ta bashin Naira tiriliyan 7.3.

Wane mataki Tinubu ya dauka kan bashin NNPC?

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya kafa kwamiti don kawo karshen matsalar da ke tsakanin Hukumar Asusun Gwamnati da Rarraba Kudaden Shiga (FAAC) da kuma NNPC.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Ware Naira Dubu 245 Ga Ko Wane Mai Bautar Kasa, Ya Yi Alkwari Ga Wasu Matasan

Kwamitin ya hada da ma’aikatar kudi da hukumar FIRS da kuma hukumar NUPRC da Akanta Janar na Gwamnatin Tarayya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Tinubu tuni ya samu rahoton farko na kwamitin kan matsalar.

Tinubu ya dawo da tallafi bayan biyan N169bn a watan Agusta

A wani labarin, ana cikin murna yayin da Shugaba Bola Tinubu ya dawo da tallafin mai a Najeria bayan cire shi a watan Mayu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Tinubu ya biya Naira biliyan 169 a watan Agusta na kudin tallafin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.