Kamfanin NNPCL Ya Yi Tankade da Rairaya, Ya Kori Manyan Jami'ai Daga Muƙamansu

Kamfanin NNPCL Ya Yi Tankade da Rairaya, Ya Kori Manyan Jami'ai Daga Muƙamansu

  • Kamfanin mai na gwamnatin tarayya (NNPCL) ya yi tankaɗe da rairaya a ɓangaren ma'aikata ranar Talata
  • A wata sanarwa da ya fitar da safe, kamfanin ya kori manyan ma'aikatan da ya rage musu ƙasa da watanni 15 su yi ritaya
  • Wannan mataki na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan NNPCL ya sauya mataimakan shugabansa guda uku

FCT Abuja - Kamfanin man fetur na gwamnatin Najeriya (NNPCL) ya kori manyan ma’aikatansa waɗanɗa ke da ragowar ƙasa da 15 gabanin yin ritaya.

Matakan yi wa ma'aikatan ritayar dole na ƙunshe a wata sanarwa da kamfanin NNPCL ya wallafa a shafinsa na dandalin Tuwita wanda aka sauya wa suna zuwa X ranar Talata.

Kamfanin mai na ƙasa NNPCL.
Kamfanin NNPCL Ya Yi Tankade da Rairaya, Ya Kori Manyan Jami'ai Daga Muƙamansu Hoto: NNPCL
Asali: Facebook

NNPCL ya sauya mataimakan shugaba

Wannan ci gaban na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da kamfanin ya sanar da tsige mataimakan shugaban uku (EVPs) tare da maye gurbin su nan take.

Kara karanta wannan

Manyan Hadiman Gwamna da Wasu Jiga-Jigai Sun Ƙara Yi Wa PDP Babban Lahani, Sun Koma APC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadanda Tankaɗe da rairayar baya ta shafa sun hada da Abdulkabir Ahmed, wanda ya kasance mai kula da ɓangaren iskar gas, wuta da sabbin makamashi.

Sai kuma Adokiye Tombomieye, wanda ya jagoranci bangaren sama da kuma Adeyemi Adetunji, wanda shi ne mai kula da harkokin da suka shafi ƙasa.

Kamfanin ya maye gurbinsu da Olalekan Ogunleye a matsayin EVP na gas, wuta da sabbin makamashi; Oritsemeyiwa Eyesan a ɓangaren ayyukan kamfanin na sama, yayin da Adedapo Segun ya karɓi ragamar gudanar da aikin ƙasa.

Meyasa kamfanin ya ƙara korar manyan ma'aikata?

A wata ‘yar gajeruwar sanarwa da ya fitar a safiyar ranar Talata, kamfanin NNPC ya bayyana cewa sabon garambawul ɗin ya yi daidai da burinsa na farfado da ɓangaren ma’aikata.

Sanarwan ta ce:

"A kokarinmu na gina sabuwa kuma nagartacciyar tawaga domin tallafawa da cika manufofin kasuwancinmu, ya zama wajibi mu sake farfado da ma'aikatan mu."

Kara karanta wannan

Majalisar Dokokin Jihar Kano Za Ta Gwangwaje Mai A-Daidaita-Sahun Da Ya Mayar Da N15m, Da Muhimmin Abu 1

"Saboda haka, baya ga sauya mataimakan shugaban kamfani su uku kwanan nan, sauran manyan ma'aikata masu gudanarwa da ke da ƙasa da watanni 15 gabanin ritaya a doka za su bar kamfanin daga ranar 19 ga Satumba 2023."

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabbin Hadimai 18 a Ofishin Kashim Shettima

A wani labarin na daban Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin sabbin hadimai 18 a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima.

Tinubu ya amince da nadin masu ba da shawara na musamman da manyan mataimaka 18 domin aiwatar da kudirin gwamnatinsa a sassa daban-daban na tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262