Wasu Masu Gidajen Mai Sun Rage Farashin Lita Zuwa 430 Ga Masu Babura Da Adaidaita Sahu A Borno

Wasu Masu Gidajen Mai Sun Rage Farashin Lita Zuwa 430 Ga Masu Babura Da Adaidaita Sahu A Borno

  • Wasu daga cikin masu gidajen mai a Maiduguri sun fara siyar da mai cikin rahusa ga masu ababan hawa da babura
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta kaddamar da bas bas don rage wa mutane radadin cire tallafin mai
  • Masu adaidaita sahu da babura sun koka kan rashin ciniki wanda attajiran su ka rage farashin litar mai daga Naira 630 zuwa 420

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Borno - Wasu masu taimakon al'umma sun rage farashin litar mai a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Ragin ya shafi masu adaidaita sahu ne da kuma masu achaba a birnin bayan gwamnatin jihar ta samar da bas bas don tallafawa mutane, Legit ta tattaro.

Masu gidajen mai sun rage farashin mai zuwa N430 a Borno
Yadda wasu masu gidajen mai su ka rage farashin mai ga masu babura a Borno. Hoto: freemixer.
Asali: Getty Images

Meye ya jawo rage farashin mai a Borno?

Gwamna Babagana Zulum ya kaddamar da motocin ne guda 70 wanda ke karbar Naira 50 a wurin fasinja.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Wa 'Yan Najeriya Babban Alkawari Guda 1, Ya Ce Ko Za A Tsane Shi Sai Ya Gyara Kasar

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kaddamar da motocin ne don rage farashin sufuri a jihar wanda hakan kuma ya shafi harkokin masu adaidaita sahu da babura.

Attajirai bayin Allah sun rage farashin mai din daga Naira 620 ko wace lita zuwa 430 don masu babura da adaidaita sahu.

Leadership ta tattaro cewa wani daga cikin masu gidan mai din, Ibrahim Jibrin Muhammad ya ce ya samu karfin gwiwar yin hakan ne daga matar shugaban kasa, Remi Tinubu.

A ina ake shirin sake rage farashin mai din?

Muhammad ya ce zai yi wannan taimako a yankuna 6 na kasar da su ka hada da Legas da Kano da Rivers da Enugu da kuma Abuja.

Ragin farashin a wasu gidajen mai a Maiduguri ya samu halartar masu babura da adaidaita sahu wadanda su ka cika gidan mai din don dibar garabasa.

Kara karanta wannan

Fusatattun Matasa Sun Lakadawa Wani Mugun Duka Kan ‘Sace Mazakuta' a Abuja

Wasu daga cikin wadanda su ka ci gajiyar sun yabawa masu gidajen mai din inda su ka ce taimakon ya zo a dai-dai ganin irin halin da ake ciki.

Tinubu ya dawo da tallafin mai

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya dawo da tallafin mai yayin da ya biya Naira biliyan 196.4 a watan Agusta da ta gabata.

Tinubu ya dauki wannan matakin ne don tabbatar da farashin litar mai ta tsaya a yadda ta ke kan Naira 620 madadin kara tsada a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel