Gobara
Wata mummunar gobara ta halaka yan gida daya su bakwai sannan ya jefa al’ummar unguwar Tudun Wada da ke karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano cikin alhini.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta sanar da tashin mummunar gobara a yankin Gezawa da ke jihar. Haka kuma ta ce an yi asarar kayayyaki na miliyoyin naira.
An samu iftila'in gobara wanda ya yi ajalin mutum daya tare da lalata dukiyoyi a ma'ajiyar bakin mai da ke birnin Kano a yau Litinin 8 ga watan Janairu.
Hukumar kashe gobara ta tarayya ta sanar da fara daukar ma'aikata, an nemi 'yan Najeriya da suka cancanta da su nemi aikin ko za su dace. Mako shida za a rufe shafin
Gobara ta kone gidan marigayi shugaban jam'iyyar PDP a jihar Akwa Ibom, Obong Udo Ekpenyong. Matar marigayin da surukarsa sun riga mu gidan gaskiya.
An shiga wani yanayi bayan wata mummunar gobara ta yi sanadin shaguna fiye da 30 yayin da aka tafka asarar fiye da miliyan 300 a wata kasuwa a jihar Anambra.
Hukumar kashe gobara ta jihar Oyo ta tabbatar da cewa gobara ta lakume gidan tsohon gwamnan Oyo, marigayi Adebayo-Akala. Mutum biyu sun mutu, daya ya jikkata.
Hukumar jami'an kwana-kwana ta jihar Kano ta tabbatar da tashin gobara a sakateriyar ƙaramar hukumar Gwale da safiyar ranar Laraba, ta laƙume ofisoshi 17.
An samu tashin gobara har sau biyu a jihar Kwara. Gobarar wacce ta tashi daban-daban a rukunin shagunan ta kona shaguna guda 17 da lalata dukiyoyi.
Gobara
Samu kari