Gwamnatin Zamfara Ta Fadi Abin da Za Ta Yi Wa Wadanda Gobara Ta Ritsa da Su a Gusau

Gwamnatin Zamfara Ta Fadi Abin da Za Ta Yi Wa Wadanda Gobara Ta Ritsa da Su a Gusau

  • Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal ta waiwayi ƴan kasuwar da gobara ta ritsa da su a Gusau
  • Gwamna Dauda Lawal ya sha alwashin bayar da tallafi ga ƴan kasuwar domin su farfaɗo daga asarar da suka yi
  • Gwamnan ya kuma miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga shugabannin kasuwar da iyalan mutum ɗaya da ya rasa ransa a sakamakon gobarar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yi alƙawarin bayar da duk wani tallafi da taimako ga waɗanda gobarar babbar kasuwar Gusau ta shafa.

A daren ranar Talata ne wata gobara ta tashi a babbar kasuwar Gusau, inda ta yi sanadiyar mutuwar mutum ɗaya da lalata shaguna sama da 50.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya fadi babban dalili 1 da ya sa ya dakatar da fitaccen basarake a jiharsa

Gwamnatin Zamfara za ta ba da tallafi
Gwamnatin Zamfara za ta ba ƴan kasuwar da gobara ta ritsa da su a Gusau tallafi Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce a lokacin da ake tantance irin barnar da gobarar ta yi, gwamna Lawal ya sha alwashin taimakawa waɗanda lamarin ya shafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa Gwamna Lawal ya tabbatar wa mutanen da abin ya shafa da iyalansu cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don rage musu raɗaɗin da suke ciki da kuma taimaka musu su farfaɗo.

Gwamna Dauda ya yi wa ƴan kasuwar jaje

Da yake jawabi ga waɗanda gobarar ta shafa a babbar kasuwar Gusau, gwamnan jihar Zamfara ya jajanta wa shugabannin kasuwar bisa rasuwar mutum ɗaya a dalilin gobarar.

A kalamansa:

"Ina miƙa ta’aziyyata ga shugabannin kasuwar da kuma iyalan mamacin da ya rasu sakamakon gobarar da ta faru a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta haɗa kai da gwamnan APC domin su yi maguɗi a jihar Arewa? Gaskiya ta bayyana

"Tun kafin afkuwar gobarar da ta faru, na kafa wani kwamiti da zai gudanar da cikakken bincike kan yadda gwamnati za ta shigo domin inganta da bunƙasa kasuwannin jihar nan.
"Gwamnatina ta ƙuduri aniyar tallafawa waɗanda gobarar ta shafa kuma za ta binciko hanyoyi daban-daban don rage musu asarar."

Gwamna Dauda Ya Ƙaddamar da Rundunar Tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ƙaddamar da sabuwar rundunar tsaro a jihar.

Gwamnan ya ƙaddamar da rundunar ne domin yaƙi da ƴan bindiga da ƴan ta'adda a faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel