Abun Bakin Ciki Yayin da Yan Gida Daya Mutum 7 Suka Mutu Sakamakon Gobara a Kano

Abun Bakin Ciki Yayin da Yan Gida Daya Mutum 7 Suka Mutu Sakamakon Gobara a Kano

  • Wata mummunar gobara da ta tashi ta yi sanadiyar rasa yan gida daya su bakwai a Tudun Wada, karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano
  • An tattaro cewa abun bakin cikin ya faru ne sakamakon tartatsin wutar lantarki yayin da mamatan ke cikin bacci a daren ranar Lahadi, 14 ga watan Janairu
  • Jami'in hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf, ya ce hayakin da ya tashi daga gobarar ne ya turnuke mamatan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Wani mummunan al'amari ya riski al'ummar yankin Tudun Wada, karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano yayin da gobara ta lakume rayukan yan gida daya mutum bakwai.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, majiyoyi sun ce tartatsin wutar lantarki ne ya haddasa gobarar a daren Lahadi, 14 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Tsageru sun farmaki motar kamfen mataimakin gwamnan PDP, sun tafka mummunar ɓarna

Gobara ta hallaka yan gida daya su 7
Abun Bakin Ciki Yayin da Yan Gida Daya Mutum 7 Suka Mutu Sakamakon Gobara a Kano Hoto: Fedfireng
Asali: Facebook

Yadda gobara ta lakume, uba, uwa da yaransu 5

Wani ganau, Malam Idi Maikatako, ya fada ma manema labarai a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu cewa Uba, Uwa da yaransu gaba daya sun mutu a cikin baccinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa daya daga cikin yaran da ya tsira yana nan kwance a asibiti yanzu haka yana karbar magani.

Maikatoko ya ce:

"Lamarin ya afku ne a tsakar dare lokacin da mamatan ke tsaka da bacci. Mutanen da abun ya ritsa da su - Uba, Uwa da yaransu biyar sun kone kurmus yayin da dansu na shida ke kwance a asibiti.
"Lamarin ya afku ne sakamakon wani turtsatsin wuta da ya faru bayan an dawo da wutar lantarki."

Jami'in hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf, ya ce hayaki ne ya turnuke mamatan har lahira, rahoton Sahara Reporters.

Kara karanta wannan

Tsohon sanata ya shiga tashin hankali bayan 'yan damfara sun kwace WhatsApp dinsa

Yusuf ya ce:

“Mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a lamarin yayin da hayaki ya shake su. An garzaya da wadanda abin ya shafa asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsu.
"Lokacin da mutanenmu suka isa wurin, sun gano cewa an kwashe wadanda abin ya shafa zuwa asibiti sannan makwabta da bayin Allah sun kashe wutar kafin mutanenmu su isa wurin."

Gobara ta lakume dukiya a Kano

A wani labarin kuma, mun ji cewa shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Kazeem Sholadoye, ya bayyana cewa gobara ta lakume dukiya da darajarsu ta kai naira miliyan 80 a yankin Gezawa da ke jihar.

Sholadoye ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Punch a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel