Mummunar Gobara Ta Lakume Kyayyakin Naira Miliyan 80 a Kano

Mummunar Gobara Ta Lakume Kyayyakin Naira Miliyan 80 a Kano

  • Mummunar gobara ta yi barna a jihar Kano inda aka rasa dukiyoyi da darajarsu ta kai kimanin naira miliyan 80
  • Kazeem Sholadoye, Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ne ya tabbatar da hakan inda ya ce ana ci gaba da bincike don gano abun da ya haddasa tashin gobarar
  • Haka kuma, Sholadoye ya ce an yi nasarar kubutar da wasu kayayyaki da darajarsu ta kai kimanin naira miliyan 300

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Kazeem Sholadoye, ya bayyana cewa gobara ta lakume dukiya da darajarsu ta kai naira miliyan 80 a yankin Gezawa da ke jihar.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi shagube ga Betta kan alkawarinta na fitar da yan Najeriya miliyan 50 daga talauci

Sholadoye ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Punch a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu.

Gobara ta yi barna a jihar Kano
Mummunar Gobara Ta Lakume Dukiyoyin da Ya Kai Naira Miliyan 80 a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Ana binciken dalilin tashin gobarar, Sholadoye

Ya kuma bayyana cewa har yanzu ana gudanar da bincike don gano musababbin tashin gobarar sannan cewa an yi nasarar samo kayayyaki da darajarsu ya haura naira miliyan 300, rahoton Platinum Post.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Darajar kayayyakin da aka rasa a gobarai ta kai naira miliyan 80 a hasashenmu.
“Abun da jami’an da suka je wajen suka rahoto kenan, koda dai bincike na ci gaba da gudana kan abun da ya haddasa gobarar. Kayayyakin da aka ceto sun kai na naira miliyan 300.”

A wani lamari makamancin wannan, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da gobara ta cinye ma'ajiyar bakin mai a Kano.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi martani kan dakatar da Betta Edu, ya aika gagarumin sako ga Tinubu

Gine-gine da dama da ke cikin ma'ajiyar sun kone a mummunar gobarar a yankin Hotoro sa ke bayan gari.

Hukumar kashe gobara a jihar ta kawo daukin gaggawa bayan shafe awanni uku inda ta dakile gobarar.

Mutane da dama da ke kusa da inda abin ya faru sun tsare daga wurin da don tsira da rayuwarsu.

Shaidan gani da ido ya tabbatar wa Daily Trust cewa wutar ta kama ne bayan wata tanka makare da mai ta zo harabar kamfanin.

Gobara ta lakume rayuka biyu

A gefe guda, mun kawo a baya cewa a kalla mutum biyu suka mutu a wata gobara da ta tashi a gidan tsohon gwamnan jihar Oyo, marigayi Adebayo Alao-Akala.

Kwamandan hukumar kashe gobara na Obomoso, Mr Oluwaseyi Awogbile, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda gobarar ta fara karfe 7:30 na safiyar Litinin, 18 ga watan Disamba, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel