Gobara Ta Tashi a Dakin Taro na Ahmed Musa, Bayanai Sun Fito

Gobara Ta Tashi a Dakin Taro na Ahmed Musa, Bayanai Sun Fito

  • Gobara ta ƙone wani ɗakin taro na miliyoyin naira mallakin kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa
  • An tattaro cewa gobarar ta tashi ne daga wani shagon walda da ke kusa da wurin taron da ke Karji a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna
  • A halin yanzu Musa ba ya ƙasar tare da tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya inda suka halarci gasar AFCON ta 2024 a ƙasar Cote D’Ivoire

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ɗakin taron miliyoyin naira na kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa, ya ƙone a Karji, ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

A halin yanzu Musa yana tare da tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya domin halartar gasar cin kofin nahiyar Afirika ta 2024, (AFCON) a ƙasar Cote D’Ivoire.

Kara karanta wannan

Duk da wuyar da aka sha, Buhari ya fadi dalilin da ya sa ya ki korar Emefiele daga shugabancin CBN

Gobara ta tashi a dakin taron Ahmed Musa
Dakin taro na Ahmed Musa ya kone a Kaduna Hoto: Alex Morton
Asali: Getty Images

Kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito, wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa gobarar ta tashi ne daga wani shagon walda da ke kusa da ɗakin taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane waje gobarar ta shafa?

Ɓarkewar gobarar ta shafi wasu sassan harabar da ke ɗakin taron kafin makwanbtan da ke wurin su yi gagggawar kashe ta, rahoton Bleuprint ya tabbatar.

Wani mazaunin garin, Musa Dangiwa ya ce tun da aka kafa wurin, masu neman nishaɗi daga sassa daban-daban na jihar sukan yi tururuwa zuwa ɗakin taron domin shaƙatawa.

A kalamansa:

"Muna farin ciki da Ahmed Musa bisa ƙirƙirar wurin shaƙatawa a wajenmu."

Gobara ta tashi a Kasuwar Panteka

Wata mummunar gobara ta tashi a fitacciyar kasuwar Panteka da ke a Kaduna, inda ta shafi ɓangaren ƴan katako da ke kasuwar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi hanya 1 da zai bi wajen magance matsalar rashin tsaro a Najeriya

Hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna ta tabbatar da aukuwar lamarin, cikin wata sanarwa da darakanta ya fitar a birnin Kaduna.

Gobara Ta Tashi a Gidan Mai a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mummunar gobara ta jawo wani mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da ta cinye ma'ajiyar baƙin mai a birnin Kano.

Gine-gine da dama da ke cikin ma'ajiyar sun ƙone a mummunar gobarar wacce ta tashi a yankin Hotoro da ke bayan garin cikin birnin na Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel