Mummunar Gobara Ta Lakume Shaguna Masu Yawan Gaske a Babbar Kasuwar Jihar Arewa, An Rasa Rai

Mummunar Gobara Ta Lakume Shaguna Masu Yawan Gaske a Babbar Kasuwar Jihar Arewa, An Rasa Rai

  • An samu tashin wata mummunar gobara a sashin yan kayan daki da ke babbar kasuwar Gusau, babban birnin jihar Zamfara
  • Gobarar wacce ta tashi da misalin karfe 9:00 na dare ta janyo asarar dukiya mai tarin yawa bayan ta kona shaguna da dama
  • Kwamandan hukumar kashe gobara ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce wani mai shago ya rasa ransa a kokarinsa na kashe wutar ta karfi da yaji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Rahotanni sun kawo cewa mummunar gobara ta lakume shaguna da dama a babbar kasuwar garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, inda aka kuma rasa rai daya.

An rahoto cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 9:00 na daren ranar Talata, 30 ga watan Janairu, a sashin yan kayan daki da ke babbar kasuwar.

Kara karanta wannan

Jama'a sun shiga tashin hankali gobara ta kame wasu makarantun sakandare a Anambra

Gobara ta lakume shaguna a babbar kasuwar Gusau
Mummunar Gobara Ta Lakume Shaguna Masu Yawan Gaske a Babbar Kasuwar Jihar Arewa, An Rasa Rai Hoto: @FedfireNG
Asali: Facebook

Me hukumomi suka ce kan tashin gobarar?

Kwamandan hukumar kashe gobara ta Najeriya, ofishin sabuwar kasuwa, Hamza Mohammed, ya tabbatar da rasa ran mutum daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya sanar da gidan talabijin na Channels cewa wani mai shago wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba ya mutu a lokacin da yake kokarin shiga shagonsa domin kashe gobara ta karfin tuwo.

Yan kwana-kwana daga hukumar jihar suna ta kokarin kashe gobarar tun daga karfe 9:00 na dare, don hana ta yaduwa zuwa sauran shaguna.

Mohammed ya bayyana cewa gobarar ta taba shaguna masu yawan gaske, amma har yanzu ba a san musabbbabin tashin ta ba, rahoton Naija News.

Gobara ta lakume miliyoyi a kasuwar waya

A wani labari makamancin wannan, mun ji a baya cewa shaguna da dama da dukiyoyi na miliyoyin Naira ne suka lalace a daren ranar Litinin bayan da gobara ta tashi a kasuwar waya ta Damaturu a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

An tsinci gawar wani matashi babu kunne yashe a bola a wata jihar arewa

Jaridar Leadership ta tattaro cewa gobarar wacce ta tashi da misalin ƙarfe 6:23 na dare, ta ɗauki sa'o'i kafin a samu damar kashe ta.

Jami'an tsaro, ƴan kwana-kwana da jama'ar yankin ne dai suka yi haɗin gwiwa wajen kokarin ganin an kashe gobarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel