Yaki da ta'addanci a Najeriya
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an ‘yan sandan jihar Plateau sun kama wani matumi da ake zargin yana kokarin kai wa ‘yan bindiga makamai a garin Jos.
Rundunar ƴan sanda ta samu nasarar hallaka Auwalu Mahaukaci, wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya damu al'umma a kewayen karamar hukumar Ɗandume a Katsina.
A ci gaba da kokarin kawo karshen duk wani nau'in ta'addanci, wani kwamandan ƴan ta'adda ya ji wuta ya miƙa wuya ga rundunar sojojin Najeriya a Kaduna.
Kotu ta sallami shugaban Miyetti Allah Kautal Kore Bello Bodejo daga tuhumar da ake masa na ta’addanci wanda ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya ya shigar.
Wasu yan ta’adda a jihar Kaduna sun gamu da gamonsu bayan hadakar jami’an tsaro suka fatattake su a maboyarsu dake Karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna.
Yayin da Bola Ahmed Tinubu ke murnar cika shekara ɗaya da hawa kan madafun iko, mun tattaro yanna Najeriya ta yi fama da matsalolin tsaro a shiyyoyi shida.
Gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar da motoci 150 da babura 500 domin rabawa ga jami'an tsaro dake yaki da ta'addanci a jihar wanda gwamna Uba Sani ya kaddamar.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radɗa ya roki gwamnatin tarayya ta agazawa jami'an tsaro da nagartattun makamai domin su tunkari matsalar tsaron jihar.
Sojoji a jihar Kaduna sun yi nasarar dai-daita wasu 'yan ta'adda bayan harin kwantan-bauna da suka kai musu. An yiwa 'yan ta'addar raga-raga a yankin Kidandan.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari