"Ƴan Bindiga Sun Fara Kai Hari da Manyan Bindigu," Gwamna Radɗa Ya Tura Saƙo ga Tinubu

"Ƴan Bindiga Sun Fara Kai Hari da Manyan Bindigu," Gwamna Radɗa Ya Tura Saƙo ga Tinubu

  • Gwamnatin Katsina ta yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya taimaka domin a dawo da zaman lafiya a faɗin jihar
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Nasiru Ɗanmusa ya ce a yanzu ƴan bindiga sun fara kai hari da miyagun bindigu
  • Ya kuma jaddada cewa Gwamnatin Dikko Raɗɗa ba za ta nemi sulhu da ƴan bindiga ba, za ta ci gaba da yaƙarsu har sai zaman lafiya ya dawo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Gwamnatin Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda ta roki gwamnatin tarayya ta kawo ɗauki domin magance matsalar tsaro a jihar.

Gwamnatin ta jaddada buƙatar gwamnatin tarayya ta samar da kayan aiki masu inganci ga jami'an tsaron jihar domin su ci gaba da yaƙi da ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

"Kano ta kama hanyar kamawa da wuta," Jigo ya buƙaci Tinubu ya dakatar da Gwamna Abba

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
Yan bindiga sun fara amfani da manyan makamai masu haɗari a jihar Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

'Yan bindiga sun gawurta a Katsina

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Dakta Nasiru Ɗanmusa ne ya yi wannan kira ranar Litinin da daddare, kamar yadɗa Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi kira ga Bola Ahmed Tinubi ya kawo wa Katsina agaji ne jim kaɗan bayan taron majalisar tsaro na gaggawa karkashin jagorancin Gwamna Raɗɗa.

Gwamnati ta gano shirin ƴan bindiga

Ya ce gwamnatin jihar ta gano cewa ‘yan bindigar da ke kawo cikas ga zaman lafiyar jihar, yanzu suna amfani da manyan makamai irinsu RPG.

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin Katsina ta kudiri aniyar ci gaba da tunkarar ƴan bindigar har sai zaman lafiya ya dawo a dukkan sassan jihar.

Ya kuma bayyana cewa ba za a nemi sulhu da ƴan ta'addan ba musamman a wannan lokacin da aka rage masu ƙarfi.

Kara karanta wannan

"Mun shirya tsaf," 'Yan sanda sun ƙara ɗaukar mataki kan rigimar sarautar Kano

Ɗanmusa ya yabawa yadda aka ƙara samun haɗin kai tsakanin jami'an tsaro da gwamnati, inda ya ce suna iya bakin ƙoƙarinsu wajen ganin bayan ƴan bindiga.

Ya ce:

"Muna da kwarin guiwa game da jami’an tsaro kuma muna aiki tare a matsayin ‘yan uwa wanda hakan ma ya ba mu dama da nasarori a yaki da ƴan bindiga a jihar.
Gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba kuma gwamnanmu ya shirya tsaf don magance matsalar rashin tsaro, shi ya sa batun tsaro shi ne abu na ɗaya, na biyu da na uku da ya fi bai wa fifiko."

DHQ ta kalubalanci Dikko Radɗa

A wani rahoton kuma hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta yi martani kan zargin da gwamnan jihar Katsina ya yi na cewa wasu gurɓatattun sojoji na haɗa baki da ƴan bindiga.

DHQ ta ƙalubalanci gwamnan da ya kawo hujjojin da za su tabbatar da zargin da ya yi kan jami'an rundunar sojojin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel